Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

UBANGIJI MADAUKAKI


Muhammad Riza Muzaffar

Hafiz Muhammad Sa’id

Mun yi imani cewa Allah Madaukaki daya ne makadaici babu wani abu kamarsa, magabaci ne bai gushe ba kuma ba ya gushewa, Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai hikima, Adali, Rayayye, Mai iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abin da ake siffanta halittu da shi, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba jauhar [1] ba ne kuma ba ard [2] ba ne, ba Shi da nauyi ko sako-sako, ba Shi da motsi ko sandarewa, ba Shi da guri ba Shi da zamani kuma ba a nuni zuwa gare Shi, kamar yadda babu kini gare Shi, babu kama, babu kishiya, babu mata gare Shi, babu da, babu abokin tarayya, kuma babu wani tamka gare Shi. Gannai ba sa riskarSa Shi kuwa yana riskar gannai.
Duk wanda ya ce ana kamanta shi da halittarsa, kamar ya suranta fuska gare Shi da hannu da idaniya, ko cewar Yana saukowa zuwa saman duniya, ko yana bayyana ga ‘yan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to yana matsayin wanda ya kafirce da Shi ne wanda ya jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abin da muka bambance shi da tunanin kwakwalwarmu da sake-saken zukatanmu a mafi zurfin ma’anarsa, to shi abin halitta ne kamarmu, mai komawa ne zuwa gare mu, kamar yadda ya zo daga Imam Bakir (A.S), mamakin kyawun wannan bayani mai hikima! Mamakin wannan abin nema na ilimi mai zurfi!` .
Haka nan ana kirga duk wanda ya ce yana nuna kansa ga halittunsa ranar kiyama a cikin kafirai [3] koda kuwa ya kore masa kamantuwa da jiki, batun baka ne kawai, kuma irin masu wannan da’awa sun sandare ne a kan zahirin laffuzan Kur’ani ko hadisai, kuma suka karyata hankulansu suka yi watsi da su, suka kuma kasa yin amfani da aiki da zahiri gwargwadon yadda nazari da dalilai da ka’idojin aron kalma, da kuma ka’idojin aron ma’anar kalma suke.

Kadaita Allah (S.W.T)

Mun yi imani cewa ya wajaba a kadaita Allah ta kowace fuska kamar yadda ya wajaba a kadaita shi a zatinSa, kuma mun yi imani da cewa shi kadai ne a zatinsa da wajabcin samuwarsa, kamar yadda muka yi imani da kadaita shi a siffofi da cewa siffofinsa su ne ainihin zatinsa kamar yadda bayani zai zo game da hakan. Mun kuma yi imani da cewa ba shi da kama da shi a siffofinsa, shi a ilimi da kudura ba shi da tamka, a halittawa da arzutawa ba shi da abokin tarayya, a cikin kowace kamala ba shi da kini.
Haka nan wajibi ne a kadaita Shi a bauta, bai halatta a bauta wa waninsa ba ta kowace fuska, kamar yadda bai halatta ba a hada Shi da wani abu a nau’o’in ibada, wajiba ce ko wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma waninta na daga ibadoji. Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne, kamar wanda yake riya a ibadarsa yake neman kusanci zuwa ga wanin Allah (S.W.T), hukuncinsa da wanda yake bauta wa gumaka daya ne babu bambanci a tsakaninsu.
Amma ziyartar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau’in neman kusanci da wanin Allah a ibada kamar yadda wasu daga masu son suka ga tafarkin Shi’a Imamiyya suke rayawa suna masu jahiltar hakikanin al’amarin, shi ba komai ba ne sai wani nau’i na aiki domin samun kusanci zuwa ga Allah (S.W.T) ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusanci gare shi ta hanyar gaishe da maras lafiya, da kai jana’iza, da ziyartar ‘yan’uwa na Addini, da kuma taimakon talaka.
Don zuwa gaishe da maras lafiya Shi a kan kansa kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusanci da Allah ta hanyarsa, ba neman kusanci da maras lafiyar ba ne da zai sanya aikinsa ya zama bauta ga wanin Allah (S.W.T) ko kuma shirka a bautarSa. Haka nan sauran kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda suka hada da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da kai janaza da kuma ziyartar ‘yan’uwa.
Amma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan Addini suna daga kyawawan ayyuka a shari’a wannan al’amari ne da ya tabbata a fikihu, ba nan ne wajan tabbatar da shi ba. Abin da muke so mu yi bayani a nan shi ne; gudanar da irin wadannan ayyuka ba ya daga cikin irin nau’o’in shirka da Allah kamar yadda wasu suke rayawa, ba kuma bautar imamai ba ne, sai dai abin da ake nufi shi ne rayar da al’amuransu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah a tare da su “wannan, duk wanda Ya girmama alamomin Addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan takawar zukata”. Surar Hajj: 32.

Siffofin Ubangiji (S.W.T)

Mun yi imani cewa daga cikin siffofinsa akwai siffofi tabbatattu na hakikanin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi, da iko, da wadata, da nufi, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne da suke kari a kan zatinSa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, kudurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai kudura, babu tagwayantaka (biyuntaka) a siffofinSa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala.
Na’am siffofinsa sun sassaba a ma’anoninsu ne ba a hakikaninsu da samuwarsu ba, domin da sun kasance sun sassaba a samuwarsu, da an sami kididdigar ubangiji, kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ga ubangiji ba, wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.
Tabbatattun siffofi na idafa [4] kuwa, kamar halittawa, da arzutawa, da gabatuwa, da kuma samarwa, duk suna komawa ne a bisa hakika zuwa ga siffa guda ta hakika, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda daya wacce ake fahimtar irin wadannan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da kuma la’akari daban-daban.
Amma siffofin da ake kira salbiyya -korarru- wadanda ake kiransu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu daya, wato kore kasancewarsa mai yiwuwar samuwa [5] ba wajibin samuwa ba, abin da yake nufin kore jiki, da sura, da motsi, da rashin motsi, da nauyi, da rashin nauyi, da makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa. Sannan kuma kore kasancewarsa ba wajibin samuwa ba yana tabbatar da kasancewarsa wajibin samuwa, wajabcin samuwa kuwa yana daga cikin siffofi tabbatattu na kamala, don haka siffofin Jalala korarru a karshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah (S.W.T) kuwa makadaici ne ta kowace fuska, babu yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawa a hakikaninsa makadaici sidif.
Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra’ayin cewa siffofi tabbatttu suna komawa ne zuwa ga siffofi salbiyya, saboda ya kasa gane cewa siffofin Allah su ne ainihin zatinsa, sai ya yi tsammanin cewa siffofi tabbatattu suna komawa zuwa korewa ne domin ya samu nutsuwar imani da kadaitakar zati da rashin kididdigarsa, amma sai ya fada cikin abin da yake mafi muni saboda sanya ainihin zati wanda shi ne ainihin samuwa, kuma tsantsar samuwa wanda ba shi da wata nakasa ko wata fuska ta siffar yiwuwar samuwa. Sai ya sanya shi ya zama aininin rashi kuma tsantsar korarre[6], Allah ya kiyayye mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma zamewar duga-dugai.
Kamar yadda mamaki ba ya karewa ga wanda yake da ra’ayin cewa siffofinSa na subutiyya -tabbatattu- kari ne a kan zatinSa, ya yi imani da kididdigar zatin Allah wajibin samuwa, da samuwar ababan tarayya [7] gareshi, ko kuma wannan magana tasa ta kai shi ga imani da hauhawar zatinsa madaukaki.
Shugabanmu Amirul Muminin (A.S) ya ce:
Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi [8], saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuwa ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya kididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: A kan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin [9].

Adalcin Allah

Mun yi imani cewa yana daga siffofin Allah madaukaki tabbatattu na kamala cewa shi adali ne ba azzalumi ba, ba ya take hakki a shari’arsa ba ya zalunci a hukuncinsa, yana saka wa masu biyayya kuma yana da hakkin hukunta masu sabo, ba ya kallafawa bayinsa abin da ba zasu iya ba, kuma ba ya yi musu ukuba fiye da abin da suka cancanta.
Kuma mun yi imani cewa Ubangiji ba ya barin aikata abu mai kyau matukar ba wani abin da zai hana aikata shi, kuma ba ya aikata mummuna saboda Shi mai kudura ne a kan ya aikata kyakkyawa ko ya bar mummuna, tare da cewa yana da sani game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna, da wadatuwarSa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan, babu wani kyakkyawan (aiki) da aikata shi zai cutar da Shi balle ya bar shi, babu kuma wani mugun aiki da yake bukatarsa balle ya aikata shi, tare da cewa shi mai hikima ne ba makawa aikinsa ya kasance ya dace da hikima kuma a bisa tsari mafi kamala.
Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki to da al’amarin hakan ba zai rabu da daya daga cikin surorin nan hudu ba:
1- Ya kasance ya jahilci al’amarin bai san cewa mummuna ba ne.
2- Ko kuma ya kasance ya san da shi amma an tilas ta shi a kan aikata shi, ya kuma gajiya ga barin aikata shi.
3- Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata shi ba, bai kuma gajiya ga barin sa ba, sai dai yana bukatar aikatawa.
4- Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba a kuma tilasta shi ba, ba ya kuma bukata gareshi, sai al’amarin ya takaita ke nan a kan cewa aikisa ya zama bisa sha’awa da wasa.
Dukkan wadannan surori sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi, alhali Shi tsantsar kamala ne, saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakke ne daga zalunci da kuma aikata abin da yake mummuna.
Sai dai kuma wasu sashen musulmi sun halatta wa Allah (S.W.T) aikata mummuna, suka halatta cewa zai iya azabtar da masu biyayya, ya kuma shigar da masu sabo aljanna kai hatta kafirai ma, kuma suka halatta cewa yana iya dora wa bayinsa abin da ya fi karfinsu da abin da ba zasu iya ba, tare da haka kuma ya azabtar da su a kan ba su aikata ba. Kuma suka halatta zalunci da danne hakki, da karya da yaudara ga Allah madaukaki, da kuma aikata aikin da babu wata hikima, da manufa, da maslaha, da fa’ida, da hujjar cewa shi: “Ba a tambayar sa a kan abin da yake aikatawa amma su ana tambayar su”. Surar Anbiya: 23.
Da yawa daga cikin irin wadannan da suka suranta Shi a kan wannan Akida tasu batacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, Ja’iri, mai wauta, mai wasa, makaryaci, mai yaudara, da yake aikata mummunan aiki yana barin kyakkyawa, Allah ya daukaka ga aikata wadannan abubuwa daukaka mai girma, wannan shi ne kafirci tsantsansa [10].
Kuma Allah Madaukaki yana cewa: “Kuma Allah ba ya nufin zalunci ga bayi”. Surar Mumin: 23. “Kuma Allah ba ya son barna”. Surar Bakara: 31. “Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abin da ke tsakaninsu muna masu wasa ba”. Surar Dukhan: 205. “Kuma ban halicci aljani da mutum ba sai don su bauta mini”. Surar Zariyat: 56. Da sauran ayoyi masu girma, tsarki ya tabbata gareka ba ka halicci wannan don barna -rashin manufa- ba

Hukuncin Allah A Kan Baligi

Mun yi imani cewa Allah (S.W.T) ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu da hujja a kansu, kuma ba ya kallafa musu sai abin da zasu iya aikatawa, da abin da zasu iya masa, da abin da suka sani, domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, da jahili maras takaitawa wajan neman sani.
Amma shi kuwa Jahili mai takaitawa wajan neman sanin hukunce-hukunce, shi wannan abin tambaya ne wajan Allah, kuma abin yi wa azaba ne a kan takaitawarsa da sakacinsa, domin ya wajaba a kan kowane mutum ya nemi sanin abin da yake bukata gareshi a sanin hukunce-hukuncen shari’a.
Kuma mun yi imani cewa: Babu makawa Allah madaukaki ya kallafa wa bayinsa ayyuka ya kuma sanya musu shari’o’in abin da yake na maslaharsu da alherinsu da rabautarsu ta har abada, ya kuma gargade su ga barin abin da yake akwai barna da cutuwa a kansu da mummunan karshe gare su, koda kuwa ya san cewa su ba zasu bi Shi ba, domin wannan tausasawa ce da kuma rahama ga bayinSa domin su suna jahiltar mafi yawancin maslaharsu da hanyoyin samunta a nan duniya da kuma lahira. Suna kuma jahiltar da yawan abubuwan da zasu jawo musu cutarwa da tabewa, Shi kuwa Ubangiji Shi ne Mai Rahama mai Jin kai, kuma Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa da yake mustahili ne ya rabu da shi har abada.
Ba ya janye wannan tausasawa da wannan rahama domin kasancewar bayinsa sun bujire wa bin sa, sun ki bin abubuwan da ya yi umarni da abubuwan da ya hana.

Hukuncin Allah Da Kaddara

Mujabbira [11] sun tafi a kan cewa Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan halittu, sai ya zamanto ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma ya yi musu azaba, kuma ya tilasta su a kan aikata abin da ya yi umarni tare da haka ya ba su lada, domin sun tafi a kan cewa ayyukansu tabbas ayyukanSa ne, ana dai danganta ayyukan ne garesu saboda rangwame domin su ne mahallin ayyukan Ubangiji. Asalin wannan kuwa domin su sun yi inkarin sababi na dabi’a tsakanin abubuwa [12], suna ganin Allah madaukaki ne yake aikata komai bisa hakika.
Sun yi musun wannan sababi ne saboda tsammanin cewa hakan shi ne ma’anar kasancewar Ubangiji mahalicci, wanda ba Shi da abokin tarayya, amma duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa hakika ya danganta zalunci ga Allah, Shi kuwa ya tsarkaka daga hakan.
Mufawwada [13] kuma sun yi imanin cewa Allah ya sallama ayyuka ne ga halittu, ya janye kudurarsa da hukuncinsa da kuma kaddarawarsa daga gare su, da la’akari da cewa; danganta ayyukan gare shi yana nufin dangata nakasa gare shi ne, kuma halittu suna da nasu sababan na musamman duk da cewa dukkansu suna tukewa ne zuwa sababi guda daya na farko wanda shi ne Allah (S.W.T). Duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa, hakika ya fitar da Allah daga mulkinSa ya kuma yi shirka da shi da halittunSa.
Abin da muka yi imani da shi a nan muna masu biyayya ga abin da ya zo daga lmamanmu tsarkaka da suke cewa al’amari ne tsakanin al’amura biyu, al’amarin da irin wadannan masu jayayya daga malaman ilimin sanin Allah suka kasa fahimtarsa, wasu kuma suka takaita, wasu kuma suka zurfafa, babu wani daga cikin masana ilimi da ma’abuta falsafa da ya fahimce shi sai bayan karnoni masu yawa.
Ba abin mamaki ba ne ga wanda bai tsinkayi hikimar Imamai (A.S) dangane da al’amari tsakanin al’amura biyu ba, ya yi tsammanin cewa wannan magana ta al’amari ne tsakanin al’umara biyu tana daga abin da malaman falsafa na turai na wannan zamani suka gano, alhali kuwa Imamanmu sun rigaye su tun kafin karnoni goma da suka wuce.
Imam Sadik (A.S) ya fada yana mai bayanin hanyar nan matsakaiciya da cewa: “Babu Tilastawa kuma babu fawwalawa sai dai al’amari ne tsakanin al’amuran guda biyu.
Wannan kalma ta girmama! ma’anarta ta zurfafa! A takaice abin nufi shi ne; hakika ayyukanmu a bangare guda ayyukanmu ne bisa hakika kuma mu ne sababinsu na dabi’a kuma suna karkashin ikonmu da zabinmu, a daya bangaren kuma suna karkashin kudurar Allah ne kuma suna cikin karkashin mulkinsa, domin Shi ne mai ba da samuwa mai bayar da ita, bai tilasta mu a kan ayyuka ba ballantana ya zama ya zalunce mu idan ya yi mana azaba a kan sabo, domin muna da iko da kuma zabi a kan abin da muke aikatawa. Kuma bai fawwala mana samar da ayyukanmu ba ballantana ya zamanto ya fitar da su daga karkashin ikonsa ba, al’amarin halittawa da hukuntawa da umarni duka nasa ne, kuma shi mai iko ne a kan komai kuma masani da bayinsa.
Ta kowane hali, imaninmu shi ne hukuncin Allah da kaddarawarsa sirri ne daga asiran Allah (S.W.T) duk wanda ya iya fahimtarsa yadda ya dace ba tare wuce gona da iri ba ko kuma takaitawa ba, to wannan ya yi, in ba haka ba, bai wajaba a kansa ba ya kallafawa kansa fahimta da zurfafawa a cikinsa ba, domin gudun kada ya bata, akidarsa ta lalace, domin wannan yana daga al’amura masu zurfi, kai yana daga mafi zurfin bahasosin falsafa wadanda ba mai gane so sai daidaikun mutane, kuma duga-dugan da yawa daga malaman ilimin akida sun zame, kallafa wa kai fahimtarsa, kallafa wa mutum maras ilimi mai zurfi ne da abin da yake sama da ikonsa.
Saboda haka ya wadatar mutum ya yi Imani da shi a dunkule kawai yana mai biyayya ga fadin Imamai tsarkaka (A.S) cewa; shi wani al’amari ne tsakanin al’amura biyu, babu tilastawa babu kuma fawwalawa a cikinsa, kuma shi ba ya daga cikin shika-shikan akida ballantana kudurcewa da shi dalla-dalla da zurfafawa su zama wajibi ko ta halin kaka.

Aikin Allah Da Canzawa

“Bada” ga mutum; shi ne wani sabon ra’ayi ya bayyana gare shi wanda a da can bai kasance yana da wannan ra’ayin ba, wato ya canja niyyarsa da ya yi a kan wani aiki da ya kasance yana nufin aikata shi domin faruwar wani abu gareshi da zai sanya canji a ra’ayinsa da saninsa, sai ya canja niyya sai ya bar aikata shi bayan da can yana nufin ya aiwatar da shi, wannan kuwa ya faru ne sakamakon jahiltar maslaha da kuma yin nadama a kan abin da ya gabata.
“Bada” da wannan ma’anar mustahili ne ga Allah (S.W.T) domin kuwa yana daga jahilci ne da nakasa, wannan kuwa ya koru ga Ubangiji, kuma Shi’a Imamiyya ba su yarda da shi ba. Imam Sadik (A.S) ya ce: “Wanda ya yi da’awar cewa canji cikin wani abu ya faru ga Allah (S.W.T) game da wani abu canji irin na nadama, to a gurinmu wannan ya kafirta da Allah mai girma”. Kuma ya ce: “Wanda ya raya cewa wani abu na canjin ra’ayi ya faru ga Allah wanda ya kasance bai san shi ba jiya to ka barranta daga gareshi”.
Sai dai kuma akwai wasu hadisai da aka ruwaito daga Imamanmu wadanda suke kusan nuni da ma’anar “Bada” kamar yadda ta gabata, kamar yadda ya zo daga Imam Sadik (A.S) cewa: “Wani abu bai taba bayyana ba ga Allah kamar yadda ya bayyana gareshi game da Isma’ila dana”. Don haka ne wadansu daga marubutan musulmi suka danganta Bada ga Shi’a Imamiyya da waccan ma’ana domin suka ga mazhaba kuma tafarki na Ahlul Baiti (AS), suka sanya wannan daya daga abubuwan da suke suka da aibata shi’a da shi.
Sahihiyar magana a nan ita ce, mu muna fadi kamar yadda ubangiji ya fada a littafinsa ne cewa: “Allah yana shafe abin da ya so kuma yana tabbarwa kuma Ummul kitab a gunsa take ”. Surar Ra’ad: 39.
Abin nufi shi ne cewa Allah (S.W.T) na iya bayyanar da wani abu ta harshen Annabinsa ko waliyyinSa ko kuma a zahiri saboda wata maslaha da ta sanya bayyanawar, sa’annan daga baya sai ya shafe shi ya zama ba abin da ya bayyana da farko ba, kamar yadda ya faru a kissar Annabi Isma’il (A.S) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S) Ya ga yana yanka shi a mafarki. A nan sai ma’anar maganar Imam Sadik (A.S) ta zama cewa: Babu wani abu da ya bayyana ga Allah (S.W.T) a kan wani abu kamar yadda ya bayyana gare shi a kan Isma’ila dansa yayin da ya dauki ransa kafin rasuwar Imam Sadik (A.S) domin mutane su san cewa shi Isma’ila ba Imami ba ne, bayan a zahiri ya riga ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa.
Wani abu da yake kusa da ma’anar “Bada” shi ne shafe hukunce-hukuncen shari’o’in da suka gabata da shari’ar Annabinmu Muhammadu (S.A.W) da kuma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen da Annabinmu (S.A.W) ya zo da su.

Hukunce-hukuncen Addinin Allah

Mun yi imani cewa Ubangiji ya sanya hukunce-hukunce wajibai da haram da sauransu daidai da maslaha da alheri ga bayinSa a cikin ayyukansu, abin da maslaharsa ta zama tilas sai ya sanya shi wajibi, wanda kuma cutarwar da take tare da shi ta kai matuka sai ya haramta shi, wanda kuwa maslaharsa a garemu ta zama mai rinjaye ya soyar da shi - mustahabbi- a garemu.
Wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarsa ga bayinsa, kuma babu makawa ya zamanto yana da hukunci a kan kowane al’amari, babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto ba shi da hukuncin Allah a kansa koda kuwa hanyar saninsa ta toshe garemu. Kuma hakika yana daga mummuna ya zama ya yi umarni da abin da yake akwai barna a cikinsa, ko kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Sai dai wasu daga daga cikin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne abin da Ubangiji ya hana kawai, kyakkyawa kuwa shi ne abin da ya yi umarni da shi, babu wata maslaha ko cutuwa a cikin ayyukan su a kan-kansu, wannan magana kuwa ta saba wa hukuncin hankali.
Kamar yadda suka halatta wa Allah ya aikata mummuna ya yi umarni da abu wanda akwai cutarwa a cikinsa, kuma ya hana abin da yake akwai maslaha a cikinsa. Hakika ya gabata cewa wannan magana akwai ketare iyaka mai girma a cikinta, ba domin komai ba sai domin lizimta danganta jahilci da gazawa ga Allah (T.A.U.K).
A takaice dai abin da yake ingantacce a yi imani da shi, shi ne : Ubangiji madaukaki ba shi da wata maslaha ko amfani a cikin kallafa mana wajibai da hana mu aikata haram, maslahar wannan duk tana komawa zuwa garemu ne, babu wata ma’ana wajen kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni da su ko hani ga barin su, domin Allah ba ya hani kara zube don wasa, kuma shi mawadaci ne ga barin bayinsa.


1. Abin da yake bai damfara ko dogara da wuri ba.
2. Abin da yake ya damfara ko ya dogara da wuri.
3. Karfici a nan ba irin wanda yake fitar da mutum daga musulunci ba ne kamar yadda yake sananne cewa kafirci matakai-matakai ne.
4. Siffofin Idafa su ne siffofin da suke nuna alaka tsakanin bangare biyu, wato bangaren Allah da kuma na bayinsa, kamar arzutawa da halittawa.
5. Shi ne wanda samuwarsa daga waninsa take wato shi abin halitta ne.
6. Wannan ra’ayi ne na daya daga malaman mu’utazila da mabiyansa, abin da yake nufi shi ne, siffofin tabbatar da kamala ga Allah suna komawa ga kore tawaya ne, kamar idan aka ce mai iko ne to awajansu abin da ake nufi shi ne ba gajiyye ba ne, amma wai ba a iya cewa ma’anar ta mai iko ne, domin gudun kada a kamanta shi da bayinsa. A lokacin da wannan ra’ayi ya kai su ga tauye Allah (S.W.T) domin idan aka ce mai ilimi yana nufin ba jahili ba amma kuma ba ya nufin ma’anar mai ilimi, wannan a gun mu mazhabar imamiyya isna ashariyya tauye Allah ne da kore masa kamala, Allah ya tsare mu daga kaucewar tunani.
7. Wannan ra’ayi ne na Ash’ariyya da suke ganin siffofin ma’ani ba kawai ma’ana ba ne da Allah shi ne hakikanisnsu na zahiri kamar yadda sauran siffofinsa suke, suna ganin wadannan siffofi suna da tabbatattun hakikaninsu a zahiri na hakika da suke siffantuwa da su, misali kamar Ali da yake da sunaye ne da siffofi, da za a ce masa Ali dan Muhammad, baban Isa, dogo ne, kuma kakkaura, sai a ce siffofinsa dan Muhammad, baban Isa, da dogo, da kakkaura, duk a zahiri suna da daidaikun da suke siffantuwa da su, sai ya zama Ali shi yana nuni izuwa gareshi ne kawai banda sauran siffofi, sauran siffofi kuwa suna da nasu samammu na zahiri da suke siffantuwa da su. Da maganar Ash’ariyya gaskiya ne da a nan Allah ya zama guda takwas, kamar yadda a misalinmu Ali zai zama su biyar, wato Ali, da dan Muhammad, da baban Isa, da dogo, da kuma kakkaura.
8. Wato siffofn kari guda bakwai da masu wannan nazari suka ce su ba Allah ba ne amma sun dadu ga zatin Allah kuma zatin yana bukatarsu a ra’ayin Ash’ariyya kamar yadda ya gabata a bayaninmu, da kuma Siffofin khabariyya; kamar hannun Allah, da idonsa, da fuskarsa, da suke da tawili da ma’anar da laraba suka sani alokacin saukra da littafin kur’ani mai girma, Sifffofin khabariyya siffofi ne wadanda ake tawilinsu kamar tawilin hannu da karfi ko iko ko alkawarin Allah, kamar yadda ya zo da kinayoyi da kalmomin aro a kur'ani mai girma.
9. Alhalin Allah yana ko'ina bai kebanta da wani wuri ba.
10. A sani masu wannan ra’ayi suna magana ne a matakin yiwuwa a hankalce saboda musunsu ga rawar da hankali zai iya takawa a wannan fage, amma a aikce ba su siffanta shi da wannan miyagun siffofi ba sai da lazimin maganarsu, wato sakamakon abin da suke fada suka kuma tafi a kai zai kai ga siffanta Allah da miyagun siffofin tawaya irin wadannan a hankalce.
11. Su ne mutanen da suka tafi a kan cewa ayyukan bayi a bisa hakika ayyukan Allah ne ba tare da wani tawili ba a kan haka, don haka Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan bayi kai tsaye.
12. Mujabbira, da Ash’ariyya suna da wannan ra’ayi da aka san shi da jabar na musun wasida tsakanin Allah da ayyukan da ya halitta ba. Sun musa abin da ya sanya shi tsakaninsa da bayinsa da falalarsa. Misali kamar ‘ya’yan mangwaro da suke zuwa daga itace, sai suka ce kai tsaye Allah ne ya halitta su ba tare da wata rawa da shuka a matsayinta na wasida ta taka ba, wannan shi ne kwatankwacin ayyukan bayinsa a wajansu, don haka kai tsaye ayyukansu ayyukansa ne.
13. Mu’utazilawa sun saba da Mujabbira da Ash’ariyya, su sun tafi akan Tafwidi da ma’anarsa take nufin cewa; babu hannun Allah a cikin ayyukan bayi ko kadan, wannan ra’ayi da shi da na farkon duka a gun mazhabar imamiyya kuskure ne.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
5+6 =