Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

KOYARWAR AHLUL BAITI (A.S


Akidojin Imamiyya Na Allama Muzaffar

Fassarar Hafiz Muhammad Sa’id

Tarbiyyantarwar Ahlul Baiti Ga Mabiyansu

Ahlul Baiti (AS) sun sani tuntuni cewa hukumarsu ba za ta taba dawowa garesu a rayuwarsu ba, kuma su da shi’arsu zasu ci gaba da zama a karkashin shugabannin da ba su ba, wadanda suke ganin wajabcin kawar da su da dukkan wata hanyar takurawa da tsanantawa.
Don haka a bisa dabi’a suka riki “Takiyya” addini kuma dabi’a garesu, su da mabiyansu, matukar zata kare masu jininsu kuma ba zata munana wa wasu ko addini ba, saboda su iya wanzuwa a cikin wannan rutsitsi mai ruruwar fitina mai ingizawa ga kiyayya da Ahlul Baiti (AS).
Don haka ya zama tilas suka koma ga koya wa mabiyansu hukunce-hukuncen Shari’ar musulunci, da kuma fuskantar da su fuskantarwa ta Addini ta gari, da kuma sanya su kan hanya ta tafarkin zamantakewa da jama’a mai amfani, domin su zama misalai na musulmi na gari masu adalci.
Wannan dan littafi ba zai iya kawo dukkan bayanai game da tafarkin Ahlul Baiti (A.S) ba, akwai littattafan hadisai masu girma da suka dauki nauyin yada ilimin addini, sai dai ba laifi mu yi nuni da wasu da suke kama da babin akida cikin abin da ya shafi tarbiyyantarwarsu ga shi’arsu da tarbiyyar da zata kai su ga shiga cikin al’amuran zamantakewar al’umma mai amfani, suke kuma kusantar da su zuwa ga Allah madaukaki, suke kuma tsarkake zukatansu daga daudar zunubai da laifuffuka, kuma suke mayar da su adalai masu gaskiya. Kuma magana ta gabata game da takiyya da take daya daga tarbiyya mai amfani ta zamantakewarsu, kuma zamu ambaci sashen abin da ya shafe mu na wadannan ladubban a nan.

Takiyya

An ruwaito daga Imam Sadik (A.S) a sahihin hadisi cewa: “Takiyya addinina ce kuma addinin iyayena ce”. Da kuma “Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi”. Haka nan takiyya ta kasance taken Ahlul Baiti (A.S) wajen kare kai daga cutar da su da kuma mabiyansu, da kare jininsu, da kawo gyara ga halin da musulmi suke ciki, da kuma hada kansu. Takiyya ba ta gushe ba a matsayin alama da ake sanin shi’a da ita tsakanin sauran bangarori na al’ummu, kuma dukkan mutum idan ya ga alamun hatsari ga ransa ko ga dukiyarsa saboda yarda da abin da ya yi imani da shi, ko kuma bayyanar da shi a sarari, to babu makawa ya boye, ya kiyaye a guraren hatsarin, wannan kuwa abu ne da dabi’ar hankali take hukunci da shi. Kuma sannanen abu ne cewa Shi’a da lmamansu sun sha nau’o’in jarrabawa da matsa lamba na tsawon zamani da babu wata jama’a da ta sha irinta. Wannan al’amari ya tilasta su a mafi yawan lokutansu su yi amfani da takiyya, suna masu boye wa masu sabani da su, da kuma barin bayyanarwa, da suturta akidunsa, da ayyukan da suka kebanta da su, saboda abin da yake biyo bayan hakan na daga cutuwa a addini da duniya, wannan shi ne ya sanya suka bambanta da takiyya, aka kuma san su da ita.
Takiyya tana da hukunce-hukunce ta fuskacin wajabcinta da rashin wajabcinta daidai gwargwado sassabawar wuraren tsoron cutuwa da aka ambata a babobinta a littattafan fikihu. Ita ba wajiba ba ce a kowane hali, takan iya zama halal, ko saba mata ya zama wajabi ne a wasu halaye, kamar idan bayyana gaskiya da fitowa da ita sarari ya zama taimako ne ga Addini, da hidima ga Musulunci, da jihadi a tafarkinsa, to a wannan hali dukiya ba komai ba ce, kuma ba za a fifita rai ba. Takiyya tana iya zama haram a ayyukan da sukan iya kai wa ga kashe rayuka masu alfarma, ko yada karya, ko barna a Addini, ko cutarwa mai tsanani a kan musulmi ta hanyar batar da su, ko kuma yada zalunci da ketare haddi a tsakaninsu.
A kowane hali dai, takiyya a gun Shi’a ba ta mayar da su wata kungiyar asiri, domin aiwatar da rushe-rushe da ruguje-ruguje kamar yadda wasu daga cikin makiyan Shi’a marasa fahimtar al’amura suke surantawa, kuma suka ki dora wa kansu nauyin fahimtar ra’ayi ingantacce. Kamar yadda ba ta sanya Addini da hukunce-hukuncensa su zama wani sirri daga asiran da bai halatta a bayyana su ga wanda ba ya imani da su ba, al’amarin bai zama haka ba, alhalin littattafan mazhabar Imamiyya da rubuce-rubucensu na fikihu, da hukunce-hukunce, da bahasosin akida, sun cika gabas da yamma, sun ma wuce yadda ake tsammani daga kowace al’umma da take da wani addini.
Wadanda suke son aibata shi’a sun samu damar amfani da akidarmu ta takiyya, suka sanya ta daga abubuwan da suke sukan su da ita, kamar dai ba sa iya kashe kishirwar gabarsu sai da fille wuyayensu da takubba, da tumbuke asalinsu gaba dayansu a wadancan zamunan da suka gabata, da ya isa a ce wannan dan shi’a ne ya gamu da ajalinsa a hannun makiyan Ahlul Baiti (A.S) na daga Umayyawa, da Abbasawa, da kuma Usmaniyawa. ldan sukan mai son suka ya dogara ne da abin da yake raya rashin shar’ancinsa a addini, to mu sai mu ce masa:
Na Farko: Mu masu biyayya ne ga Imamanmu (A.S) kuma muna bin shiriyarsu ne, kuma su ne suka umarce mu da ita suka wajabta ta a kanmu a lokacin bukata, ita tana daga addini a wajensu, kuma ka ji fadin Imam Sadik (A.S) da yake cewa: “Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi.”
Na biyu: Shar’anta ta kuma ya zo a Kur’ani mai girma, da fadarsa madaukaki: “Sai dai wanda aka tilasta shi alhalin zuciyarsa kuwa tana nutse da imani”. Surar Nahli: 106. Wannan aya ta sauka ne game da Ammar Dan Yasir da ya fake da bayyana kafirci saboda tsoron makiyan Musulunci. Da kuma fadinsa madaukaki: “Sai dai in kuka ji tsoron su don kariya”. Surar Ali Imran: 28. Da kuma fadinsa: “Kuma wani mutum daga mutanen fir’auna yana mai boye Imaninsa Ya ce”. Surar Gafir: 28.

Ziyartar Kaburbura

Ziyarar kaburburan -Annabi da na Imamai- da katange su da kuma yin gine-gine a kansu suna daga cikin al’amuran da Shi’a suka kebantu da su, kuma suna sadaukar da dukkan abu mai tsada da mai sauki a cikin imani da dadin rai.
Wannan kuwa asalinsa yana komawa ne zuwa ga wasiyyar Imamai da zaburar da mabiyansu kuma da kwadaitar da su a kan irin ladan da yake da shi mai yawa a gurin Allah madaukaki, saboda kasancewarta daga mafifitan ayyukan biyayya da kusanci da Allah bayan ayyukan ibadu wajibai, da kuma cewa kaburburan suna daga cikin mafifitan guraren amsa addu’a da yankewa zuwa ga Allah (S.W.T).
Kuma sun sanya wannan daga cikin cika alkawura ga Imamai, domin ga kowane imami akwai alkawarinsa a kan wuyan mabiyansa, kuma ziyartarsu tana daga mafificin cika alkawari, duk wanda ya ziyarce su yana mai kwadayin haka da gaskata abin da suka kwadaitar a kai, to zasu kasance masu cetonsa a ranar lahira [1].
Akwai fa’idoji masu yawa na Addini da zamantakewa a cikin ziyartar kaburbura da suka sa Imamanmu himmantuwa da ita, domin bayan dada karfin soyayya da mika wuya da kauna tsakanin imamai da mabiyansu, hada da sabunta ambatonsu da tuna kyawawan dabi’unsu, da jihadinsu a tafarkin gaskiya, tana kuma hada musulmi daban-daban wadanda suke warwatse a waje daya domin su san juna, kuma ta dasa ruhin mikuwa zuwa ga Allah a cikin zukatansu, da yankewa zuwa gare shi da bin umarninsa, tana cusa musu hakikanin tauhidi a cikin ma’anonin addu’o’in ziyarorin da suke cike da fasaha wadanda aka samo daga Ahlul Baiti (AS), tare da koya musu tsarkin musulunci da sakonsa, da abin da ya wajaba a kan musulmi na daga dabi’u madaukaka, da kaskan da kai ga mai tafiyar da al’amuran halitta (S.W.T), da gode wa ni’imominsa, don haka ta wannan bangaren tana amfani ne irin na addu’o’in da aka ruwaito wadanda bayaninsu ya gabata. Wasunsu ma suna dauke da sama da haka, kuma mafi daukakarta kamar ziyarar “AminulLahi” wacce take ziyara ce da aka rawaito daga Imam Zainul Abidin (A.S) yayin da ya ziyarci kabarin kakansa imam Ali (A.S).
Kamar yadda wadannan ziyarorin da aka ruwaito suke fahimtar da matsayin imamai (AS) da irin sadaukarwarsu a tafarkin taimakon gaskiya, da daukaka kalmar Addini da kadaitarsu ga ibadar Allah (S.W.T), ga shi kuma sun zo da salon larabci mai fasaha madaukakiya, da ma’anoni masu sauki wadanda kowa yake iya fahimta, kuma suna kunshe da mafifitan ma’anonin tauhidi masu zurfi, da addu’a, da yankewa zuwa gare shi madaukaki. Hakika tana daga cikin mafi ingancin ladubban Addini bayan Kur’ani mai girma da Nahjul Balaga da kuma addu’o’in da aka ruwaito daga garesu (AS), domin a cikinta akwai takaitaccen bayanin sanin Imamai (AS) game da abin da ya shafi sha’anin Addini da gyaran zuciya a dunkule.
Sannan a cikin ladubban ziyarar akwai koyarwa da shiryarwar da ke karfafa tabbatar da samuwar wadannan dabi’u na Addini madaukaka, wanda ya hada da daukaka tsarkin ruhin musulmi, da yaduwar tausasawa ga fakiri, da iya zamantakewa da al’umma, da son cudanya da jama’a, domin daga ladubbanta akwai abin da ya kamata a aikata kafin a fara shiga cikin ginin makabartar domin ziyartarsa.
Daga nan kuma akwai abin da ya kamata a yi a tsakiyar ziyarar, da kuma bayan ziyarar, da mu a nan zamu bujuro da sashen wadannan ladubban domin fadakarwa kan manufarta da muka ambata:
1- Daga ladubbanta, mai ziyarar ya yi wanka yayin fara ziyararsa ya tsarkaka, fa’idar wannan kuwa cikin abin da muka fahimta a fili take, ita ce mutum ya tsarkake jikinsa daga dauda, domin ya kubutar da shi daga rashin lafiya da cututtuka, kuma domin kada mutane su gundura [2] da warinsa, ya kuma ya tsarkake kansa daga kazanta. Hakika ya zo a cikin hadisai cewa; mai ziyara ya karanta wannan addu’a bayan ya kare wanka domin fadakar da shi game da wadancan manufofi madaukaka, sai ya ce: “Ya Allah ka sanya mini haske da tsarki tare, da kuma tsari mai isarwa ga dukkan cuta da ciwo da dukkan aibi, kuma ka tsarkake zuciyata, da gabobina, da kasusuwana, da namana, da jinina, da gashina, da fatata, da bargona, da kashina, da kuma abin da kasa ta dauke shi daga gare ni, kuma ka sanya mini halarta ranar bukatata da fakirancina da talaucina.”
2- Ya sanya mafi kyawu kuma mafi tsaftar tufafin da yake da su, domin sanya kyawawa da tsaftatattun tufafi a taron jama’a abu ne da mutane suke so wa junansu, kuma yake kusantar da su ga junansu, tare da kara musu daukaka da jin daukaka a bukin da suke halartarsa.
Daga abubuwan da suka kamata mu jawo hankali garesu a wannan koyarwa su ne, ba a wajabta wa mai ziyara sanya mafi kyawun tufafi baki daya ba, sai dai ya sanya mafi kyawun abin da zai iya, domin ba kowa ne zai iya yin haka ba, kuma akwai takurawa ga talakawa, al’amarin da tausayawa ba ta bukatar a yi haka, sai ya zamanto ya hada tsakanin wannan tarbiyya da abin da ya kamata na kawa da kuma kiyaye halin talaka da mai raunin hali.
3- Ya sanya turare matukar yana da shi, wannan fa’idarsa tamkar ta sanya sababbin tufafi ce.
4- Ya yi sadaka ga fakirai da abin da ya saukaka gare shi, kuma fa’idar sadaka a irin wannan al’amari sananniya ce, domin a cikin hakan akwai taimaka wa gajiyayyu, da kuma karfafa ruhin tausasawa gare su.
5- Ya tafi yana mai nutsuwa da kwanciyar hankali, mai runtse ganin idonsa, abin da yake cikin irin wannan nutsuwar na girmama alfarmar wannan gurin, da kuma wanda ake ziyarta, da fuskanta zuwa ga Allah madaukaki, da yankewa zuwa gare shi, ba boyayye ba ne, tare da abin da hakan ya kunsa na nisantar damun mutane da matsa musu a yayin wucewa, da kuma rashin munana wa sashensu ga sashe.
6- Ya yi kabbara da fadin: “Allahu Akbar” ya yi ta maimaitawa yadda ya so, a wasu ziyarorin an kayyade kabbarorin zuwa dari. Akwai fa’idar jin rai ga girman Allah a cikin yin haka, da kuma cewa ziyara ba komai ba ce sai bauta ga Allah da girmama shi da tsarkake shi ta hanyar raya alamomin Allah da karfafa Addininsa.
7- Bayan kammala ziyarar ga Annabi ko ga Imami sai ya yi salla mafi karanci raka’a biyu domin bauta ga Allah da godiya gareshi saboda dacen da ya yi masa, ya kuma bayar da ladanta ga wanda ya kai wa ziyarar. A cikin addu’ar da aka ruwaito wacce mai ziyarar zai karanta bayan wannan salla akwai abin da zai fahimtar da mai ziyarar cewa, wannan sallar tasa da aikinsa duk don Allah ne shi kadai, da kuma cewa shi ba ya bauta wa waninsa, ziyarar ba wata abu ba ce sai wani nau’in neman kusanci zuwa gareShi madaukaki.
“Ya Uabangiji gareka na yi salla, gare ka na yi ruku’u, gareka na yi sujada, kai kadai ba ka da abokin tarayya, domin salla da ruku’u da sujada ba sa kasancewa sai gareka, domin kai hakika kai ne Allah babu abin bautawa sai kai. Ya Uabangiji ka yi tsira da aminci ga Muhammad da zuriyar Muhammad kuma ka karbi ziyarata, ka kuma ba ni abin da na roka, domin Muhammad da zuriyarsa masu tsarki.”
A cikin irin wannan nau’in na ladabi, akwai abin da yake bayyana wa wanda yake son fahimtar hakikanin manufofin Imamai (A.S) da mabiyansu masu koyi da su a ziyartar kaburbura, da kuma abin da yake toshe bakin masu nuna jahilta da suke raya cewa, ziyarar kaburbura ibada ce gare su da neman kusanci gare su, kuma shirka ce da Allah. Abin zato a nan shi ne cewa, hadafin wadannan shi ne, nesantar da jama’a daga abin da yake jawo wa jama’ar imamiyya amfanin zamantakewa da na addini a bukukuwan ziyara, domin ya zama tsakuwar ido ga masu kiyayya da Ahlul Baiti (A.S), in ko ba haka ba, ba ma tsammanin wadannan mutane suna jahiltar hakikanin manufar Ahlul Baiti (A.S), mustahili ne ga wadannan da suka tsarkake niyyarsu ga Allah, suka kadaitu da ibada, suka bayar da rayukansu wajan taimakon addini, su kira mutane zuwa ga shirka da Allah.
8- Daga ladubban ziyara akwai cewa: Mai ziyara ya lizimci kyautata abotakar wanda yake tare da shi, da karanta magana sai dai da ta alheri, da yawaita ambaton Allah, da kaskan da kai, da yawaita salla, da salati, da runtse idanuwansa, kuma ya taimaka wa mabukata daga cikin yan’uwansa idan ya ga guzirinsu sun yanke, da taimaka musu, da tsantseni kan abin da aka hana, da kuma husuma, da yawaita rantsuwa da jayayya [3].
Sannan hakikanin ziyara ba komai ba ne sai salati ga Annabi (S.A.W) da Alayensa, da la’akarin cewa “Su rayayyu ne ana arzuta su gun Ubangijinsu”. Kuma suna jin magana suna amsawa, kuma ya isa ya ce: Assalamu alaika ya RasulalLah! Sai dai abin da ya fi, ya karanta abin da aka rawaito na hadisai da suka zo game da ziyara daga Ahlul Baiti (A.S), saboda abin da yake cikinta na daga manufofi madaukaka da fa’idoji na addini, tare da balagarta da fasaharta, da kuma abin da yake cikinta na daga addu’o’i madaukaka da mutum yake fuskanta zuwa ga Allah makadaici a cikinta.

Raja’a (Komowa Duniya)

Abin da Mazhabar Ja’afariyya Imamiyya ta tafi a kansa da riko da abin da ya zo daga Ahlul Baiti (A.S) Shi ne cewa; Allah (S.W.T) zai komo da wasu mutane daga cikin wadanda suka mutu zuwa duniya a bisa kamanninsu da suka kasance a kai, sai ya daukaka wasu ya kuma kaskantar da wasu, ya dora masu gaskiya a kan marasa gaskiya, ya kuma saka wa ababan zalunta daga azzalumai, wannan kuwa zai faru ne yayin bayyanar Mahadi (A.S).
Ba mai dawowa sai wanda darajarsa ta imani ta daukaka ko kuma wanda ya kai kololuwa a barna, sannan sai su sake mutuwa, daga baya kuma sai tashin kiyama, sai kuma samun sakamakon abin da suka cancance shi na kyakkyawan sakamako ko kuma azaba, kamar yadda Allah ya kawo a cikin Kur’ani mai girma game da burin da wadanda suka komo din wadanda suka sami fushin Allah suke yi domin a dawo da su dawowa ta uku ko sa gyara ayyukansu: “Suka ce Ya Ubangijinmu ka matar da mu sau biyu kuma ka rayar da mu sau biyu, to mun yi furuci da zunubanmu, shin akwai wata hanyar fita”. Surar Mumin: 11.
Na’am Kur’ani ya zo da yiwuwar komowa zuwa duniya hadisai da dama sun zo daga Ahlul Baiti (A.S) game da hakan, kuma mabiya Ahlul Baiti sun yi ittifaki a kan haka in ban da ‘yan kadan daga cikinsu da suka yi tawilin abin da ya zo game da Raja’a da cewa, ma’anarta ita ce komowar hukuma da umarni da hani a hanuun Ahlul Baiti (A.S), da bayyanar lmamin da ake sauraro ba tare da komowar wasu ayyanannu mutane ba ko rayar da matattu.
Batun Raja’a kuwa a gurin Ahlussunna yana daga cikin abin ki da imani da shi ya munana, kuma marubutansu a ilimin sanin maruwaitan hadisai suna kirga imani da raja’a abin suka ga mai ruwaya, kuma aibi gare shi da yake wajabta kin ruwayarsa da jefar da ita, tayiwu suna kirga ta a matsayin kafirci da shirka ne ko ma tafi muni, don haka wannan yana daga cikin mafi girman abubuwan da suke sukan Shi’a da aibata su da shi.
Babu shakka wannan wata barazana ce da kungiyoyin Musulmi a tsawon zamani suke amfani da ita domin sukar sashensu, kuma ba mu ga wani abu da zai janyo wannan ba, domin imani da Raja’a ba ya rushe imani da tauhidi ko Annabci, yana ma kara inganta su ne, domin Raja’a dalili ne a kan kudurar Allah cikakkiya kamar yadda tashin kiyama da tayar da matattu suke. Raja’a tana daga cikin abubuwan da suka saba wa al’ada wacce ya inganta ta zama mu’ujiza ga Annabinmu Muhammad (S.A.W) da Alayensa, kuma ita tamkar mu’ujizar rayar da matattu ce da ta kasance ga Annabi Isa (A.S), kai ta fi ta ma, domin ita tana kasancewa ne bayan matattun sun zama rididdigaggu. “Ya ce wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu? Ka ce wannan da ya fare su tun karon farko shi ne zai rayar da su, kuma shi masani ne da dukkan halittu”. Surar Yasin: 79-87.
Amma wanda ya soki Raja’a kuwa bisa dalilin cewa tana daga cikin “Tanasuhi [4]”, wannan saboda bai fahimci bambanci tsakanin “Tanasuhi” da tayar da matattu da jikkunansu na ainihi ba ne, ita Raja’a wani nau’i ne na tayar da matattu da jikinsu ne, domin ma’anar Tanasuhi ita ce: Ciratar wata rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba. Wannan kuwa ba ita ce ma’anar tayar da matattu da jikkunansu na ainihi ba, ma’anarta ita ce; komo da ainihin jikin da siffofinsa na kashin kansa da suka kebantu da shi, haka nan ma Raja’a take. Idan kuwa da “Raja’a” “Tanasuhi” ce, to rayar da matattu ta hannun Annabi Isa (A.S) ma ya zama “Tanasuhi” ne, haka ma tayar da matattu da komo da ainihin jikkunansu ya zama “Tanasuhi’’ ke nan.
Saboda haka babu abin da ya rage sai tattaunawa game da “Raja’a” ta fuska biyu.
(1) Na farko: Cewar ita mustahiliya ce.
(2)Na biyu: Karyata hadisan da suka zo game da ita.
(1)A bisa kaddarawar cewa tattaunawar guda biyu daidai ne, to yin imani da ita ba a daukarsa a matsayin kyamar da masu gaba da Shi’a suka mayar da ita, kuma da yawa daga cikin abubuwan da suke mustahilai ne wasu bangarorin musulmi suka yi imani da su, ko kuma wadanda sam ingantaccen nassi bai tabbata ba game da su, amma ba su wajabta kafirtawa da fitarwa daga Musulunci ba. Akwai Misalai masu dama a kan hakan, kamar imani da yiwuwar rafkanwa ga Annabi (S.A.W) ko kuma aikata sabo, da kuma imani da rashin farko ga Kur’ani, da kuma batun narkon azaba, da kuma imani da cewa Annabi bai yi wasiyya da halifa a bayansa ba.
Kuma wadannan munakashoshi biyu ba su da wani asasi na inagnci, amma batun cewa raja’a mustahili ce mun riga mun kawo cewa ita nau’i ce na tayar da matattu da jikkunansu, sai dai cewa tayarwa ce a nan duniya, kuma dalilin yiwuwar ta shi ne dalili a kan yiwuwar tashin kiyama. Kuma babu wani dalili a kan cewa dole ta zama abin mamaki, sai dai kawai mu ba mu saba da ita ba ne a rayuwarmu ta wannan duniya, ba mu san kuma sabubbanta da abubuwan da suke hana ta ba da zasu sanya yin ikrari da ita ko mu kore ta. Tunanin mutum ba ya saukake masa yarda da abin da bai saba da shi ba cikin sauki, kamar wanda yake mamakin tayar da matattu yana mai cewa: “Wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”. Aka ce masa: “Wannan da ya fare su tun karon farko shi ne zai rayar da su, kuma shi masani ne da dukkan halittu”. (Yasin: 78-79)
Na’am a kan makamancin wannan da ba mu da dalili na hankali a kai na tabbatar da shi ko kore shi, ko kuma mu ka raya rashin samuwar dalili, to a nan ya zama dole a kanmu mu koma wa nassosin Addini wadanda suke su ne tushen wahayin Ubangiji. Kuma abin da zai tabbatar da yiwuwar Raja’a ga wasu matattu a duniya ya zo a Kur’ani kamar dai mu’ujizar Annabi Isa (AS) ta rayar da matattu: “Kuma Ina warkar da Wanda aka haifa makaho kuma Ina rayar da matattu da izinin Allah”. Surar Ali Imran: 49.
Da kuma fadin Ubangiji: “Ta yaya Allah zai rayar da wadannan bayan mutuwarsu, sai Allah ya matar da shi Shekara dari sannan ya tayar shi”. Surar Bakara: 259.
Da kuma ayar da ta gabata da take cewa: “Suka ce Ya ubagijinmu Ka matar da mu sau biyu”. Surar Mumin: 11. Ma’anar wannan ayar ba zata yi daidai ba, ba tare da komowa duniya bayan mutuwa ba, duk da wasu daga masu tafsiri sun kallafa wa kawukansu yin tawilin da ba zai kashe kishirwa ba, kuma ba zai tabbatar da ma’anar ayar ba.
(2) Tattaunawa ta biyu:- Ita ce da’awar cewa hadisai game da Raja’a kagaggu ne, ba ta da asasi, domin Raja’a tana daga cikin al’amuran da suke na larura da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) na hadisai mutawatirai.
Bayan wannan, ashe ba ka yi mamakin shahararren marubucin nan mai da’awar sani Ahmad Amin a Littafinsa na Fajrul Islam, da yake cewa; “Yahudanci ya bayyana a cikin Shi’anci ta hanyar imani da Raja’a”. Don haka ni nake cewa masa: “Ashe kenan Yahudanci ma ya bayyana a Kur’ani saboda batun Raja’a”. Kamar yadda ya gabata game da ayoyin Kur’ani mai girma da suka ambaci Raja’a.
Kuma zamu kara masa da cewa: A hakika babu makawa wasu akidun Yahudanci da Kirintanci su bayyana a cikin da dama daga akidu da hukunce-hukuncen musulunci, domin Annabi mai girma (S.A.W) ya zo yana mai gaskata Shari’o’i da suka gabata, duk da yake an shafe wasu daga hukunce-hukuncensu. Don haka bayyanar Yahudanci da Kiristanci a wasu abubuwan da musulunci ya yi imani da su ba aibu ba ne cikin musulunci, wannan idan har an kaddara cewa Raja’a tana daga akidojin Yahudawa kenan kamar yadda wannan marubucin yake da’awa.
Ko yaya dai, Raja’a ba tana daga cikin shika-shikan musulunci ba ce da ya wajaba a kudurce ta da yin bincike a kanta, imaninmu da ita bi ne ga hadisai ingantattu da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) wadanda muka yi Imani da kubutarsu daga karya, kuma tana daga cikin al’amuran gaibi da suka ba da labari game da ita, kuma aukuwarta ba mustahili ba ne.

Kira Zuwa Ga Hadin Kai A Musulunci

An san Ahlul Baiti (AS) da kwadayinsu a kan wanzuwar addinin musulunci, da kira zuwa ga daukakarsa da hada kan mabiyansa, da kiyaye ‘yan’uwantaka a tsakaninsu, da cire mugun kuduri daga zukatansu, da kullace-kullace daga rayukansu, ba za a mance da matakin Amirul Muminin Aliyyu dan Abi Dalib (AS) game da halifofin da suka gabace shi ba, duk da fushin da ya yi da su da kuma yakininsa da kwacewarsu ga hakkinsa, amma sai ya tafi tare da su, ya zauna lafiya da su, kai an boye ra’ayinsa na cewa shi ne wanda aka yi wasiyya da halifancinsa, har ya zama bai bayyana nassin ba a bainar jama’a har sai da al’amarin ya koma hannunsa, sannan ya kafa hujja da sauran wadanda suka rage daga cikin Sahabbai game da al’amarin nassin Al-Ghadir a ranar Rahba da ta shahara. Ya kasance ba ya boye shawara garesu game da abin da ya shafi musulmi ko musulunci na amfani da maslaha, saudayawa yana fada game da wannan al’amari: “Sai na ji tsoron idan ban taimaki musulunci da ma’abotansa ba zan ga gibi a cikinsa ko rushewa”.
Kamar yadda babu wani abu da ya taba zowa daga gareshi wanda zai yi tasiri a karfafa mulkinsu, ko raunana jagorancnsu, ko rage kwarjininsu, sai ya kuntata wa kansa, ya zauna a gida duk da abin da yake gani daga gare su. Dukkan wannan saboda kiyaye maslahar musulunci ta gaba daya, da kiyaye kada a ga wani gibi a musulunci ko rushewa, har aka san haka daga gare shi, kuma halifa Umar dan Haddabi ya kasance yana fada yana kuma maimaitawa: “Kada na kasance cikin wani al’amari mai wuyar sha’ani da Abul Hasan ba ya ciki.” Ko fadinsa: “Ba don Ali (A.S) ba da Umar ya halaka”.
Haka nan ba za a mance da matakin Imam Hasan dan Ali (AS) ba dangane da yin Sulhu da Mu’awiya, bayan ya ga cewa dagewa a kan yaki zai shafe ya kuma kawar da Alkawari mafi girma –Kur’ani- da adalci har ma da musulunci daga samuwa har zuwa karshen zamani, a kuma shafe shari’ar Ubangiji, a kuma gama da wadanda suka yi saura daga Zuriyar Manzo daga Ahlul Baiti, sai ya fifita kiyaye zahirin musulunci da sunan Addini, duk da ya yi sulhu da Mu’awiya babban makiyin Addini da ma’abotansa, mai husuma mai mugun kuduri ga imam Hasan (A.S) da shi’arsa, tare da abin da ake tsammani na faruwar zalunci da kaskanci gareshi shi da mabiyansa, ga kuma takubban Banu Hashim da na shi’arsa a zazzare ba sa son komawa ba tare da sun yi aikinsu na kariya da gwabzawa ba, sai dai maslahar musulunci madaukakiya ita ce ta fi dukkan wadannan al’amuran.
Amma Shahidi Imam Husain (AS) idan ya motsa to domin ya ga cewa idan aka ci gaba da halin da ake ciki, Banu Umayya ba su sami wanda zai tona asirinsu ba, to da sannu zasu shafe sunan Musulunci, su kawar da darajarsa, sai ya so ya tabbatar wa tarihi ketare iyakarsu, ya fallasa abin da suke kulla wa Shari’ar Manzon Allah (S.A.W). Ba don yunkurinsa mai albarka ba, da Musulunci ya zama wani labari ne da tarihi zai rika ambatonsa tamkar wani addinin barna. Kwadayin Shi’a a kan raya ambatonsa ta hanyoyi daban- daban ya zamanto saboda kammala sakon da yunkurinsa na dauki-ba-dadi da zalunci ne, kuma domin raya al’amarinsa na cika umarni da biyayya ga Imamai (A.S) [5].
A nan kwadayin Ahlul Baiti (A.S) na wanzuwar izzar musulunci zata bayyana garemu koda kuwa mai mulki ya kasance mafi tsananin makiyansu ne a matakin Imam Zainul Abidin (A.S) da sarakunan Banu umayya alhalin sun maraita shi, an keta alfarmarsa a lokacinsu, kuma yana mai yawan bakin cikin a kan abin da suka yi wa babansa da Ahlin gidansa a waki’ar karbala, amma duk da haka yana yi wa rundunar musulmi addu’a da nasara, musulunci kuma da izza, musulmi kuma da yalwa da aminci, kuma ya riga ya gabata cewa makaminsa kawai wajen yada ilimi Shi ne addu’a, ya koya wa Shi’a yadda zasu yi addu’a ga sojojin Musulunci da musulmi, kamar addu’arsa da aka sani da “Addu’ar masu dakon iyaka” wacce yake cewa a cikinta: Ya Allah! ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muhammad, ka yawaitasu, ka kaifafa makamansu, ka kare matattararsu, ka kange iyakarsu, ka hada taronsu, ka shirya al’amarinsu, ka kadaita da wadatar da bukatunsu, ka karfafa su da cin nasara, ka taimake su da hakuri”. Zuwa inda yake cewa: “Ya Allah ka karfafa guraren Musulunci da haka, ka kiyaye gidajensu da shi, ka yawaita dukiyarsu da shi, ka shagaltar da su gabarin yakarsu don su dukufa ga ibadarka, da hana kai musu farmaki don su kadaita da kai, har ya zamanto ba a bauta wa kowa a bayan kasa sai kai, kuma ba a sanya wa goshi kasa saboda wani sai kai.” Haka nan ya ci gaba da addu’arsa mai fasaha, -kuma tana daga mafi tsawon addu’o’insa- wajen fuskantar da sojojin musulmi zuwa ga abin da ya kamace su na daga kyawawan dabi’u, da kuma shirya kansu, da tanadi a kan makiya, ta kunshi dukkan darussan yaki na jihadin Musulunci da bayanin manufarsa da fa’idarsa, kamar kuma yadda take fadakar da musulmi da irin gargadi da takatsantsan dangane da makiyansu, da abin da ya wajaba su yi riko da shi a mu’amalarsu da kariyar kansu, da kuma abin da ya wajaba a kansu game da yankewa daga komai zuwa ga Allah baki daya, da nisantar abubuwan da ya haramta, da yin abu saboda girman zatinsa.
Haka nan sauran imamai (A.S) a matakansu da suka dauka game da sarakunan lokutansu, duk da sun sami takurawa daga garesu iri-iri, da kuma azabtar da su da dukkan nau’i na kekasar zuciya da tsanantawa, domin su yayin da suka san cewa hukumar adalci ba za ta dawo hannunsu ba, sai suka juya zuwa ga koya wa mutane al’amuran Addininsu, suna fuskantar da mabiyansu fuskantarwa ta addini madaukaki. Dukkan wani yunkuri da ya faru a zamaninsu daga bangaren Alawiyyawa da wasunsu, bai kasance da ishararsu da son su ba, ya ma saba wa umarninsu da karfafawarsu ne a fili, duk da cewa sun fi kowa kwadayin kafa hukumar musulunci hatta sun fi Abbasawa son haka su kansu.
Ya isa garemu mu karanta wasiyyar Imam Musa Alkazim (AS) ga shi’arsa: “Kada ku kaskantar da kawukanku da barin biyyyar shugabanku, idan ya kasance mai adalci to ku roki Allah wanzuwarsa, idan kuwa ya kasance azzalumi to ku roki Allah gyaransa, domin gyaruwarku na cikin gyaruwar shugabanku, kuma shugaba adali yana matsayin uba mai rahama ne, ku so masa abin da kuke so wa kanku, kuma ku ki masa abin da kuke ki wa kanku”[6].
Wannan ita ce matukar abin da ake siffantawa na kiyayewar al’umma ga amincin shugaba da su so masa abin da suke so wa kansu, su ki masa abin da suke ki wa kansu.
Bayan duk wannan muna cewa: Alhakin shi’a da wasu marubuta na wannan zamani suke dauka ya girmama! Yayin da suke siffanta shi’a da cewa ita kungiya ce ta asiri mai barna, ko kuma wata jama’a ce ta ‘yan juyin juya hali. Haka nan cewa wajibi ne a kan mabiyin koyarwar Ahlul Baiti (A.S) ya ki zalunci, da azzalumai, da fasikai, ya yi duba zuwa ga mataimakansu duba na kyama, da rashin yarda, da wulakanci, wannan dabi’a ba ta gushe ba suna gadonta jikoki da ‘ya’ya, amma sam ba ya daga dabi’arsu su yi yaudara ko cin amana, kuma ba tafarkinsu ba ne yin juyin juya hali, ko su yi tawaye a kan jagorancin da yake an kafa shi da sunan musulunci, ko a boye ko a sarari.
Kuma ba sa halattawa kansu kisan gilla ko afka wa musulmi ko wace irin Mazhaba ko Darika yake bi, wannan kuwa domin rikonsu ne da koyarwar Ahlul Baiti (A.S), kuma duk musulmin da ya yi kalmar shahada biyu a wajansu, dukiyarsa da jininsa kubutattu ne, kuma cin mutuncinsa haramun ne; “Dukiyar mutum musulmi ba ta halatta sai da son ransa”. Musulmi dan’uwan musulmi ne, kuma yana da hakkoki a kansa kamar yadda bahasi mai zuwa zai yi bayani”.1. Daga maganar Imam Rida (A.S), duba littafin Kamiluz ziyarata da Ibn Kulawaih Sh: 122.
2. Tuhaful Ukul: sh, 24.
3. Kamiluz ziyarati: shafi: 131.
4. Tanasuhi shi ne ciratar wata rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba.
5. Sun kasance suna cewa Allah ya yi rahama ga wanda ya raya al’amarinmu.
6. Alwasa’il, Kitabul amri bil ma’arufi wan nahayi anil munkari: Babi 17.

Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
1+6 =