Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |

|

AYATUL-LAHI ALLAMA SHEIKH ALI KURANI (D.Z)An haifi Sheikh Kurani a Jabal Amil (Labanon) 1944, babansa yana da alaka ta musamman da Sayyid Abdulhusain sharafuddin k.s, sannan ya fara karatun cibiyoyin ilimi da na mazhabar Ahlul Bait (a.s) da aka fi sani da “Hauza” yana karami da karfafawar Abdulhusain Sharafuddin, bayan ya gama wasu ilimomi kamar; Sarfu, da Nahawu, da Mantik, da Balaga, da Ma’ani da Bayan, da Fikihu har zuwa Sharhin Lum’a, sannan sai ya koma Najafa a 1958.
Kuma ya yi karatu wajen malamai kamar Ayatul-Lahi Muhammad takiyyi, Ayatul-Lahi Al’a Baharul Ulum, Ayatul-Lahi Muhammad Taki Irawani, da gun Mar’ja’i Ayatul-Lahi Sayyid Muhammad Sa’id Allah ya tsawaita rayuwarsu.
Kamar yadda ya karanta ilimin Kalam (Ilimin sanin Allah) a wurin Sayyid Muhammad Jamal Alhashimi Allah ya ji kansa.
Ya yi karatu mai zurfi a Fikihu da Usul da aka fi sani da Bahasul khariji gun babbn Marja’i Sayyid Abul Kasim Khu’i, da gun Sayyid Shahidi Muhammad Bakir Sadar, kuma yana daga dalibansa na kusa.
Babban marja’in nan a zamaninsa Sayyid Muhsin Hakim ya aika shi yankin Diyali a shekarar 1963 a lokuta daban-daban, sannan kuma sai a 1967 Sayyid Muhsin Hakima ya aika shi Kuwait a matsayin babban wakilinsa, bayan mutuwar Sayyid Muhsin Hakim a shekarar 1970 sai ya koma karkashin wanda ya maye gurbinsa Sayyid Khu’i da ya tabbatar da shi dai wakilinsa a Kuwait .
Ya koma Labanon 1974, sai ya cigaba da wallafa Littattafai da rubuce-rubuce, kuma ya assasa abubuwan da suke amfanar jama’a kamar masallacin Rasulul A’azam, da Asibitin Arrasulul A’azam.
Bayan cin nasarar juyin Musulunci a Iran sai ya koma birnin Kum, ya ci gaba da rubuce-rubuce karkashin Ayatul-Lahi marigayi Sayyid Gulfaigani, inda ya assasa CD din nan mai kunshe da littattafai 3000 da ake kiran sa Mu’ujam Fikihi, kuma shi ne farkon CD na kompita, mai kunshe da ilimomin mazhabin Ahlul Bait, kuma yanzu an sake editin an kara shi ya kai zuwa littattafai 4700, kuma an canja masa suna zuwa maktabatu Ahlul Baiti da ana iya bude shi ne da DBD.
A yanzu yana karkashin babban Marja’in nan Sayyid Sistani ne, yana jagorantar cibiyar Markazul Mustapha, yana nan yana ta fitar da littattafai da wasu CD na akida, daga cikin CD da suka yi akwai Mu’ujam Aka’idi mai littattafan akida 700, da kuma maudu’ai 2000 kan akida.
Yana da talifofi masu yawa; wadanda suka fi shahara akwai Ahadisul Imam Mahadi da kuma Tadwinul kur’an, da Ayatul Gadir, da Wahabiyya, da Attauhid, da Hakkul Mubin , da Intisar, da sauransu.
Yana da alaka da mutane daga nahiyoyi daban-daban, kuma kullum zaurensa cike yake da masu kawo masa ziyara. Ta namu bangaren mun yi kokarin ganin aiko wa wasu daga muminai daga Shi’a da wasu daga kwafin littattafansa, a wasu lokuta, da kuma sabon CDs na Maktabatu Ahli Bait.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
3+6 =