Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Shin akwai wasu alamomin kusancin bayyanar Halifan manzon Allah na qarshe? kuma shin masu sauraron zuwansa suna da wani lada da Allah ya ware musu sakamakon wannan aiki mai wahala?


Wasu mutane sun dauka cewa sauraro yana nufin zura wa masu barna da fasadi ido suna yada barna ba tare da an yi umarni da kyakkyawa ko hani ga mummuna ba, amma a bisa abubuwan da suka gabatawannan yana nuna mana sabanin abin da wadannan suke gani. Sauraron Imam Mahadi na hakika shi ne yake kunshe cikin motsi domin kawo gyara, domin duk sadda gyara ya karu to wannan yana nufin kusantowar wanda ake sauraro domin samun alamar karbar gyara a cikin al'umma. Don haka ne massu sarauro sukan yi kokarin da zasu iya ne domin ganin an samu gyara da kafuwar gaskiya. Duk sadda aka samu yanayi wanda yake dauke da karbar gyara to a irin wannan al'umma ne za a iya samun rayuwa ta nishadin karbuwar gyarawa.
Kuma da haka ne za a samu damar habakar imani da karfafarsa da kuma kafuwar mahangar mahadiyyanci mai karfi mai cike da albarkar sauraro. Kuma masu sauraro ba sa yarda su narke cikin fasadin da ya babaye al'umma, kai suna kokari ne ma na ganin sun kawar da wanda yake kewaye da al'ummu ne, suna masu jurewa domin yin shimfida ta tabbatar daular adalci ta Imam Mahadi (a.s).

Farin ciki ya tabbata ga wanda ya tsaya a kan tafarkin kyautatawa da sauraron bayyanar Jagoran da aka yi alkawarin zuwansa a wata rana, kuma lallai wannan wani aiki ne na lada mai girma da daraja madauakakiya da matsayi na masu sauraro na hakika ga Imam Mahadi (a.s).
Daga cikin darajoji da lada na masu wannan aiki Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Farin ciki ya tabbata ga shir'ar Imam Mahadi (a.s) wadanda suke sauraron bayyanarsa a lokacin boyuwarsa, kuma suke bin umarninsa yayin bayyanarsa, wadannan su ne masoya Allah da ba su da wani tsoro ko bakin ciki da zai same su. [1] Wace irin daraja ce da matsayi mai girma da suka kai a sanya mutum cikin masoyan Allah (s.w.t).
Imam Sajjad (a.s) yana cewa: Wanda duk ya tabbata kan wilayarmu a lokacin boyuwar Imam (a.s) to Ubangiji zai ba shi ladan shahidai dubu na yakin badar da uhud. [2] Wannan yana nuna cewa masu sauraro a wannan lokaci kamar masu yaki ne da takubba a cikin rundunar Manzon Allah (s.a.w) wadanda suka cakuda jikinsu da jinin shahada.
Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Idan wani daga cikinku -Shi'a- ya mutu a halin sauraron bayyanar Imam Mahadi (a.s) to kamar wanda yake gefen Imam Mahadi (a.s) ne a hemarsa! Sannan sai ya saurara kadan ya ce: kai yana kamar wanda ya yi yaki tare da Imam Mahadi (a.s) ne. Sannan sai ya saurara ya ce: kai yana kamar wanda ya yi yaki tare da Manzon Allah (s.a.w) ne kuma ya yi shahada. [3]
Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: Wata rana Annabin Allah (s.a.w) yana fada a cikin sahabbansa: Allah ya nuna mini 'yan'uwana! Kuma ya fada sau biyu, sai shabbansa suka ce: ya ma'aikin Allah shin mu ba 'yan'uwanka ba ne?
Sai ya ce: Haka ne, ku sahabbaina ne, amma 'yan'uwana mutane ne da zasu zo a karshen zamani su yi imani da ni kuma alhalin ba su gan ni ba! Ubangiji ya nuna mini su da iyayensu kuma ya sanar dani su… tabbatarsu a kan addininsu ya fi zafin zage kayar karangiya, kuma ya fi zafin zama kan garwashin wuta.
Wadannan su ne hasken shiriya da Ubangiji ya tseratar da su daga fitinoni masu duhu. [4]
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Farin ciki ya tabbata ga wanda ya riski Imam Mahadi (a.s) kuma ya yi koyi da shi kafin bayyanarsa, kuma ya so masoyansa kuma ya ki makiyansa, kuma ya yi imani da imaman da suka gabace shi, wadannan su ne abokaina masoyana a cikin aljanna, kuma su ne mafi daraja a guna. [5] Duba ka ga irin matsayi mai girma da suka samu wajen Manzon Allah (s.a.w), kuma suka samu sunan masoya abokai daga baki mai tsarki na madaukaki (s.a.w).
Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: Wata rana zata zo wa mutane da jagoransu zai boyu, farin ciki ya tabbata ga masu dagewa a kan soyayyarmu a wannan rana. Kuma mafi karancin ladan wadannan mutane shi ne; Ubangiji zai yi kira wannan rana ya ce: ya ku bayina, kun yi imani da gaibi (Imam Mahadi) ne kuma kun gaskata shi?! to ku yi murna da ladana mai yawa, lallai ku bayina ne, ayyukanku na karbe su, kuma na yafe kurakuranku, saboda ku ne nake saurakar da rana kan bayina, kuma nake kawar musu da bala'i, idan da babu ku a cikin mutane da azabata ta sauka kansu. [6]
Mene ne ya fi wannan girma da kyawu da daraja gun masoya Imam Mahadi (a.s) masu sauraronsa! lallai wannan al'amari nasu ya girmama kuma ya daukaka.
Imam Musa Kazim (a.s) yana cewa: Farin ciki ya tabbata ga shi'armu, su ne masu dagewa kan soyayyarmu a lokacin boyuwar Imam Mahadi (a.s), kuma masu juriya kyam a kan cutarwar makiyanmu, wadannan su ne daga garemu kuma mu ma daga garesu. Su sun yarda da biyayyarmu, mu ma mun yarda da su a matsayin shi'armu, farin cikinsu ya tabbata!! Na rantse da Allah zasu kasance a matsayi da daraja irin tamu a ranar lahira. [7]


1. Kamaluddini, j 2, babi 33, h 54, shafi: 39.
2. Abin da ya gabata, babi 31, h 6, shafi: 592.
3. Biharul anwar, j 52, shafi: 126.
4. Abin da ya gabata, shafi: 123.
5. Kamaluddini, j 1, babi 25, h 2, shafi: 535.
6. Abin da ya gabata, babi 32, h 15, shafi: 602.
7. Kamaluddin, j 2, babi 34, h 5, shafi: 43.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
3+5 =