Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Mene ne ake nufi da boyuwar imam mahadi (a.s) daga al'ummar Duniya? Ku yi mana bayaninta dalla-dalla?


Da farko zamu fara yin bayani game da buyan Imam Mahadi (a.s) wanda ya shafi yanki mai girma na tarihin rayuwarsa kafin mu yi bayani game da shi a matsayinsa na mai tseratar da dan Adam kuma karshen ajiyar Allah a bayan kasa.

Boyuwa a nan yana nufin bacewa daga ganin mutane ba rashin halarta ba, don haka ne a wannan bangaren zamu yi magana game da boyuwar Imam Mahadi (a.s) daga ganin mutane alhalin yana cikinsu, yana kuma rayuwa tare da su, wannan al’amari ne da ya zo a ruwayoyin imamai (a.s) Imam Ali (a.s) yana cewa: Na rantse da Ubangijin Ali, yana tsakanin mutane, yana zuwa gidajensu, yana kaikawo a gabashi da yammacin Duniya, yana jin maganar mutane, yana yi musu sallama, yana ganinsu ba sa ganinsa har sai alkawarin Allah ya zo. [1]

Na’ibinsa na biyu yana cewa: Imam Mahadi (a.s) yana halartar aikin hajji, yana ganin mutane, yana kuma saninsu, amma su suna ganinsa amma ba sa saninsa. [2] Wannan ya nuna yana da buya kala biyu kenan, wani lokaci ba a ganisa, wani lokaci kuwa ana ganinsa amma ba a gane shi.

Imam Mahadi (a.s) ba shi ne farkon wanda ya boyu ba a cikin bayin Allah (s.w.t), da yawa daga annabawan Allah sun boyu, wannan kuwa ba domin komai ba sai maslaha ta Ubangiji da take cikin hakan, ba maslaha ce ta su ba ko ta iyalansu, saboda haka ne buya ta zama daya daga sunnonin Allah da ta faru a lokacin annabawa kama Idris, Salih, Ibrahim, Ysufu, Musa, Shu’aibu, Iliyas, Sulaiman, Daniyal, da Isa (a.s), kowanne daga cikinsu a bisa sharudda na musamman ya boyu wasu shekaru. [3] Don haka ne ruwayoyi da suke nuna buyan Imam Mahadi (a.s) suna nuna shi ne a matsayin daya da sunnonin Allah madaukaki.

Iama Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: “Hakika Imam Mahadi (a.s) yana da buya da zai tsawaita, sai mai ruwaya ya ce: menen dalilin wannan buyan ya dan Manzon Allah (s.a.w) ? sai ya ce: Ubangiji yana son ya dora shi bisa sunnar annabawa a boyansu”. [4]

Manzon rahama yana cewa: Mahadi yana daga ‘ya’yana ne… yana da boyuwa da a cikinta za a samu dimuwa da zata mamaye mutane har sai mutane sun kauce daga addininsu, sai ya zo a wannan zamanin kamar shihabun sakib “Tauraro mai walkiyar haske” sai ya cika Duniya da adalci da daidaito kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya. [5]


1. Gaiba na Nu’umani, babi 10, h 3, sh 146.
2. Biharul anwar: j 25, babi 23, sh 152.
3. Kamalauddin, j 1, babin farko zuwa na bakwai, sh 254 – 300.
4. Biharul anwar, j 52, h 3, sh 90.
5. Kamaluddini, j 1, b 25, sh 536.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
4+8 =