Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

shin da gaske ne cewa; ruwayoyi masu yawa sun zo da bayani game da ayyukan masu sauraron bayyanar jagora? idan haka ne muna son bayanai masu muhimmanci game da su?

Tabbas bin hanyar sauraro ba tare da sanin imanin da ake sauraro ba abu ne wanda ba zai yiwu ba, kuma tabbata a kan sauraron yana da alaka da sani ko fahimta ta gari game da wannan shugaba da aka yi alkawarin zuwansa, don haka muna ganin bayan sanin Imami da sunansa, da nasabarsa haka nan kuma a san matsayinsa da darajarsa.
Abu Nasar wanda yake daga masu hidima ga Imam Hasan Askari (a.s) yana daga masu halarta wurin Imam Mahadi (a.s) kafin boyuwarsa. Sai Imam Mahadi (a.s) ya tambaye shi shin kasan imaminka kuwa?
Sai ya bayar da amsa; Na'am, kai shugabana ne kuma dan shugabana! Sai Imam Mahadi (a.s) ya ce: Ba irin wannan sanin nake nufi ba, sai Abu Nasar ya ce: ina ganin sai ka fada min nufinka. Sai Imam Mahadi (a.s) ya ce: Ni ne karshen halifan Manzon Allah (s.a.w) kuma da albarkacina ne Ubangiji yake kawar da bala'i daga iyalai da kuma shi'ata. [1] Idan sanin Jagora ya samu ga masu sauraro, to a wannan yanayi ne mai sauraro zai iya ganin kansa cikin masu tsayuwa tare da Imam (a.s) a hemarsa. Don haka sai ya shirya kansa domin tsayawa tare da Imam (a.s) a fage daya.
Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: "…Wanda ya mutu yana sanin imaminsa ba abin da zai cutar da shi, wannan al'amarin (bayyanar ta Imam) ya dade ko ya yi saurin zuwa, wanda ya mutu yana sane da imaminsa ya kasance kamar wanda yake tare da Imam (a.s) ne a dardumarsa". [2]
Muna iya cewa wannan sanin wani abu ne wanda yake muhimmi da ya zo a maganganun ma'asumai (a.s) kuma wani abu ne dole da ake nemansa ga mataimakan Imam (a.s).
Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: ….A zamanin boyuwa mai tsawo ta Imam Mahadi (a.s) masu baran zasu kasance cikin kokwanto. Sai Zurara ya ce: Idan na ga wannan zamanin mene ne zan yi?
Sai ya ce: Ka karanta wannan addu'ar: ya Ubangiji ka sanar da ni kanka domin idan ba ka sanar da ni kanka ba to ba zan san annabinka ba, ya Ubangiji ka sanar da ni Manzonka domin idan ba ka sanar da ni Manzonka ka ba to ba zan san hujjarka ba, ya Ubangiji ka sanar da hujjarka (Imami) idan ba ka sanar da ni hujjarka ba to zan bace daga addinina. [3]
Matsayin Imam Mahadi (a.s) a tsarin halittar talikai shi ne abin da har yanzu ba a kawo ba [4]; Imam Mahadi (a.s) shi ne hujjar Allah mai tsayawa matsayin Annabi (s.a.w), mai jagorantar dukkan mutane wanda biyayya gareshi wajibi ce, domin biyayyarsa ita ce biyayya ga Allah madaukaki. Daya daga cikin abubuwan da suka shafi sanin Imami shi ne sanin halayensa da siffofinsa [5] kuma wannan yana da tasiri wajen ayyukanmu da halayenmu da dabi'unmu, kuma a fili yake cewa daidai sanin mutum ga rayuwar Imami wanda yake hujjar Allah a bayan kasa, to daidai irin tasirin da zata yi a rayuwarsa sosai.

A lokacin da sanin Jagora (a.s) ya samu to a wannan lokacin za a yi bayanin abin koyi wanda yake shi ne mahallin bayyanar kamalar Ubangiji madaukaki.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Farin ciki ya tababata ga wanda ya riski Imam Mahadi (a.s) kuma ya yi imani da imamai da suka gabace shi kuma ya yi koyi da su kuma ya ki makiyansu, wadannan su ne mafi soyuwar mutane mafi daraja a wajena. [6] Da gaske ne cewa dukkan wanda ya yi takawa daibada da rayuwa mai sauki da baiwa da hakuri da kuma dukkkan halaye na kaywwan dabi'u, ya bi hanyar Imam (a.s) to lallai ne zai samu daukaka wajen Allah.
Mu sani cewa ayyuka munana su ne suke nisantar da mu daga sauraron bayyanar Imam Mahadi kuma suke jinkirta karbarmu wajen Imami (a.s) da bayyanarsa, a cikin wannan akwai gargadi daga Imam Mahadi (a.s) da yake cewa: ba abin da yake tsare mu daga garesu sai abin da yake zo mana na munanan ayyukansu, ayyukan da ba sa faranta mana rai, kuma ba su dace da shi'armu ba. [7]
Babbn burin masu sauraron daular Imam Mahadi (a.s) shi ne su kai ga kasancewa tare da hujjar Allah amma su sani wannan al'amari ba ya samuwa sai da gina kai da gaskiya da kaywwan halaye.
Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa; "Wanda yake son ya kasance daga sahabban Imam Mahadi (a.s) to ya saurare shi, kuma ya yi aiki da tsentseni da kyawawan halaye yana kuma mai sauraron [8], a fili yake cewa a hanyar saurare babu wani abin koyi da ya kai Jagora (a.s).

Abin da yake kan masu sauraro bayan sanin Imami da kuma biyayya gareshi da kuma tabbata kan sauraro, shi ne kodayaushe su kasance cikin masu alaka da Imami (a.s). Bisa hakika a kodayaushe Jagora (a.s) yana tunawa da mabiyansa kuma bai taba manta da su ba koda kuwa kiftawr ido, kuma soyayyarsa garemu ta sanya shi da kansa yana addu'a kuma ya yi umarni da yin addu'a da cewa: "ku yi addu'a sosai domin gaggauta bayyanar farin ciki". [9] kuma saudaywa gaba daya mukan yi addu'a: ya Ubangiji ka kasance ga masoyinka hujja dan Hasan, tsira da amincinka su tabbata gareshi da iyayensa a wannan lokaci da kuma kowane lokaci, mai jibantar lamarinsa, kuma mai kiyayewa, kuma jagora kuma mai taimako, kuma mai shiryarwa kuma mai kulawa, har sai ka zaunar da shi (mai matsayi) a kasarka, kuma ka jiyar da shi dadi mai tsawo a cikinta. [10]
Duk lokacin da mai sauraro na hakika zai bayar da sadaka to yakan fara tunawa ne da ni'imar samuwar Jagora, kuma yana yin tawassuli ne da shi a kowane hali, kuma mai begen ganin bayyanrsa da duba zuwa ga kyawonsa maras misali.
Yana tsananta gareni in ga halitta kai kuma ba a ganinka; [11]
Mai sauraron Jagoran Duniya (a.s) kowane lokaci kuma kowace rana yana kai kawo ne a wurare kamar masallacin Sahala da Sardab da sauransu.
Masu sauraronsa kullum suna jaddada masa bai'a ne suna daukar masa alkawari, suna masu karanta addu'a suna masu fada: ya Ubangiji ni ina jaddada masa bai'a da alkawari a kan wuyana a wannan safiya ta ranata wannan matukukar ina raye, kuma ba zan juya gabarinta ba kuma ba zan gushe ba har abada, ya Ubangiji ka sanya ni cikin mataimakansa masu kare shi, masu gaggawa zuwa gareshi don biyan bukatarsa, kuma masu bin umarninsa masu kariya gareshi kuma masu rige zuwa ga nufinsa masu shahada a gabansa. [12]
Idan da mun fahimci hakikanin abin da yake cikin wannan addu'a ba zamu taba samun rauni ba wajen tabbatare da burinmu kuma ba zamu taba ja baya ba wajen ganin mun saurari zuwansa ba.
Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: "Duk wanda ya karanta wannan addu'a kwana arba'in a jeri to zai tashi cikin mataimakan Imam Mahadi (a.s), idan ma ya mutu to Allah zai tashe shi daga kabarinsa ya taimaki Imam Mahadi (a.s).

Hada hannun wuri daya domin ganin an samu nasarar abin da yake shi ne hadafin Jagora kuma hujjar Allah yana daga cikin ayyukan da suka hau kan masu sauraronsa, don haka ne dole ne a samu al'umma mai haduwa wuri daya domin samun kafuwar daular Imam Mahadi (a.s).
Imam Mahadi (a.s) yana fada a cikin bayanansa: "Idan shi'armu suka cika alkawarin da suka dauka, kuma suka yi niyya kan hakan to ni'imar haduwa da mu ba zata yi jinkiri garesu ba, kuma za a gaggauta musu dacewar haduwa da mu da saninmu cikakke na hakika". [13] Alkawarin ya zo a cikin littafin Allah da maganar imamai masu tsarki da zamu yi nuni da mafi muhimmancinsu:
1-Kokarin biyayya ga imamai (a.s) da son masoyansu da nisantar makiyansu: Imam Muhammad Bakir (a.s) yana cewa: Farin ciki ya tabbata ga wadanda suka riski Imam Mahadi (a.s), a lokacin kafin bayyanarsa suka yi bayayya gareshi kuma suka so masoyansa kuma suka ki makiynasa, wadannan su ne abokaina a aljanna kuma abin so ne kuma masu daraja al'ummata, a ranar kiyama. [14]
2-Tsayuwa kan kyawawan halaye da dagewa wajen yakar bidi'o'i da karkacewa a addini da kuma hana yada mummuna:
Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: a karshen zamani za a samu wasu mutane daga al'ummata ladansu kamar ladan al'ummar musulumi ta farko ne, suna umarni da kyakkyawa suna hani ga mummuna kuma suna yakar ma'abota fitina. [15]
3-Taimakon raunana da binciken halayensu da taimaka musu; Wasu jama'a daga Shi'a sun nemi Imam Muhammad Bakir (a.s) ya yi musu nasiha sai ya ce: duk wanda yake mai karfi a cikinku to ya taimaki mai rauni, kuma maras bukata ya taimaki mabukaci, kuma kowannenku ya yi wa waninsa aikin alheri. [16]
4- Yada ilimin sanin Imam (a.s) a cikin al'umma, kuma da nuna halaye na Imam da koyarwarsa cikin al'umma.
Daya daga cikin sahabban Imam Muhammad Bakir (a.s) Abdulhamid wasidi yana cewa: A sauraron al'amarin bayyanar Imam Mahadi mu mun yi wakafin rayuwarmu ta yadda matsaloli zasu kasance tare da mu.
Sai Imam (a.s) ya ce: Kai Abdulhamid shin kana tsammanin cewa Ubangiji bai sanya wa wanda ya yi wakafin rayuwarsa hanyar warware matsaloli ba, na rantse da Allah ya sanya masa hanyar mafita, kuma Allah ya yi rahama ga wanda ya raya al'amarinmu. [17] Wannan yana nuna mana cewa masu sauraron Imam Mahadi (a.s) dole ne su kansace wani bangare na al'ummarsu.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
3+7 =