Shafin Farko | Gidan Littafi | Makaloli | Shubuhohi | Tambaya da Amsa | Mukabala | Masana | Masu zama Shi'a | Dakin Hotuna |
|

Shin zaku iya yi mana bayani game da ma’anar da kuke nufi da Imamanci ko jagorancin al’umma bayan annabi (S.A.W) kuma mene ne hakikaninsa, kuma mene ne siffofin imami jagora kuma halifan annabi (S.A.W)?


Mun yi imani cewa Imamanci yana daga cikin Usuluddin wadanda imani ba ya cika sai da kudurcewa da su, kuma bai halatta a yi koyi da iyaye da dangi da malamai a cikinta ba komai girmansu da darajarsu kuwa, abin da yake wajibi shi ne, a nemi sani, a yi bincike game da shi, kamar yadda ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci.
A takaice, sauke nauyin da yake kan baligi da aka wajabta masa, ya dogara ne a kan imani da imamanci tabbatarwa ko korewa, koda mun kaddara cewa imamanci ba ya cikin shika-shikan addini da ba ya halatta a yi koyi a cikinsu, duk da haka ya wajaba a yi imani da ita ta fuskacin cewa; sauke nauyin da Allah ya dora wa baligi ya wajaba a hankalce, kuma dukkaninsu ba sanannu ba ne a yanke, saboda haka wajibi ne mu koma wa wanda muka san mun sauke nauyin da yake kanmu ta hanyar biyayya gareshi, ko ya zamanto imami (A.S) a mazhabar imamiyya, ko waninsa a wasu mazhabobin.
Kamar yadda muka yi imani da cewa annabci tausasawa ce daga Allah, kuma ba makawa a kowane zamani ya kasance akwai imami mai shiryarwa da zai maye gurbin annabi a ayyukansa na shiryar da ‘yan Adam, da dora su a kan abin da yake maslaha a Sa’adar Duniya da Lahira, kuma biyayyar da Annabi ya cancanta daga mutane baki daya shi ma ya cancance ta, domin tafi da al’amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da zalunci da ketare iya daga cikinsu. A bisa wannan asasin Imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin da yake wajabta aiko da annabawa da manzanni shi ne yake wajabta sanya Imami bayan Manzo (S.A.W).
Saboda haka ne muke cewa: Imamanci ba ya taba yiwuwa sai da nassi daga Allah a bisa harshen Annabi, ko kuma a bisa harshen Imamin da ya gabata. Imamanci ba zabin kowa ba ne a tsakanin mutane, ba al’amarinsu ba ne da idan suka so zasu nada wanda suke son nadawa, ko kuma su ayyana wanda suka so ayyanawa ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan ba tare da Imami ba. Ya zo cewa: “Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu mutuwa irin ta jahiliyya” kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) a hadisi ingantacce.
A kan haka bai halatta ba wani zamani daga zamanoni ya kasance ba tare da imami da yake wajibi a yi masa biyayya ba, wanda yake ayyananne daga Allah (S.W.T), shin mutane sun ki ko ba su ki ba, sun taimake shi ko sun ki taimakon sa, sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, yana rayuwa a cikinsu ne ko kuwa yana boye ne daga idandunan mutane, domin kamar yadda ya inganta Annabi (S.A.W) ya boyu daga ganin mutane kamar yadda ya boyu a cikin kogo da shinge, haka nan yake game da imami (A.S), kuma a hankalce babu bambanci tsakanin gajeriyar boyuwa ko mai tsawo. [1]
Madaukaki ya ce: “Kuma ga kowace a’lumma akwai mai shiryarwa”. Surar Ra’ad: 8. Da kuma fadinsa: “Kuma babu wata al’umma face sai mai gargadi ya zamanto a cikinta”. Surar Fadir: 22.

Ismar Imamai

Mun yi Imani da cewa wajibi ne ga Imami ya zama katangagge daga dukkan munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da gangan ko da rafkanwa, kamar yadda annabi yake. Haka nan wajibi ne ya zama katangagge daga rafkanwa, da kuskure, da mantuwa, domin Imamai su ne masu kare shari’a, masu tsayar da ita, halinsu tamkar halin Annabi ne. Dalilin da ya hukunta mana imani da ismar annabawa kuwa, shi ne ainihin dalilin da ya hukunta mana imani da ismar Imami ba tare da wani bambanci ba.
Ba wani abu ba ne a wajan Allah
Ya sanya duniya a cikin abu daya

Siffofin Imamai

Mun yi imani cewa imami kamar yadda annabi yake, wajibi ne shi ma ya zama mafificin mutane a siffofin kamala, kamar jarumtaka, da karimci, da kame kai, da gaskiya, da adalci, da tafi da al’amura, da hankali, da hikima, da kuma kyawon dabi’u, dalilinmu na wajabcin samuwar wadannan siffofi ga Annabi shi ne dalilinmu na wajabcin siffantuwa da wadannan siffofi ga imami.
Amma game da iliminsa kuwa, shi yana samun ilmi da hukunce-hukuncen Ubangiji da dukkan saninsa ta gurin Annabi ne, ko kuma daga Imamin da ya gabace shi, Idan kuwa aka sami wani sabon abu, to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhama da karfin kwakwalwar da Allah ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al’amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure, kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka ko koyarwar malamai, duk da yake iliminsa yana iya karuwa, shi ya sa Annabi (S.A.W) a addu’arsa yake cewa: “Ubangiji ka kara mini ilimi”. [2]
Na ce: Ya tabbata a ilimin sanin halayyar dan Adam cewa kowane mutum yana da wata sa’a ayyananniya ko wasu awowi a rayuwarsa da yakan san wani abu da kansa ta hanyar kaifin fahimta wanda shi a kan kansa wannan reshe ne na ilhami, saboda abin da Allah ya sanya masa na karfin yin haka. Wannan karfi yana sassabawa da sabawar mutane a karfinsa da rauninsa, da yawansa da karancinsa. Sai kwakwalwar mutum ta kai ga sani da ilimi ba tare da ya bukaci wani tunani ba, ko kawo mukaddima da hujjoji na hankali, ko kuma koyawar malamai ba, kuma saudayawa mutum yakan sami irin haka a kan kansa a rayuwarsa, Idan kuwa al’amarin haka yake to ya halatta mutum ya kai ga kololuwar daraja da kamala a karfin tunaninsa na sanin ilhami, wannan kuwa abu ne da masana falsafa na da, da na yanzu suka tabbatar da shi.
Karfin ilhama a gun imami ana cewa da ita “kuwwa kudsiyya” wato karfi daga Allah, da take mafi kamalar kololuwar darajar ilhama, sai mai wannan siffa a kowane lokaci a kuma kowane hali ya so ya san wani abu sai ya san shi ba tare da mukaddima ba ko koyarwar wani malami, sai ya koma wa wannan abin jahiltar domin saninsa sai ya san shi tare da taimakon wannan karfi da Allah ya ba shi, sai ilimi da wannan abu ya bayyana gareshi tamkar yadda bayyanar surar abu take bayyana a tsaftataccen madubi.
Wannan kuwa abu ne bayyananne a tarihim Imamai (A.S), su a wannan fage kamar Annabi suke ba su taba yin tarbiyya ko neman ilmi a hannun kowa ba, ba su koyi karatu a gurin wani malami ba tun daga farkon rayuwarsu har zuwansu shekarun balaga, karatu ne ko kuwa rubutu, bai tabbata ba cewa daya daga cikinsu ya shiga gurin koyon rubutu ko ya yi almajiranci a hannun wani malami a kan wani abu, duk kuwa da cewa suna da matsayin ilimi da ba a iya kintatawa, kuma ba a taba tambayar su wani abu ba face sun ba da amsarsa a lokacin da aka tambaya, ba a taba jin kalmar ban sani ba daga bakinsu, ko kuma jinkirta ba da amsa har sai sun yi nazari ko tunani ko makamancinsu, alhali kuwa ba zaka taba samun wani daga cikin manyan malaman fikihu ba sai ka ji an ambaci wanda ya tabiyyatar da shi ya koyar da shi, da kuma wadanda ya karbi ruywaya ko ilimi a hannunsu, da kuma dakatawarsu a wasu mas’aloli ko kokwantosu a mafi yawa daga ilimomi, kamar yadda yake a kowane zamani da kowane guri.

Biyayya Ga Imamai

Mun yi imani da cewa Imamai su ne “Ulul’amri” Shugabannin da Allah ya yi umarni a yi musu biyayya, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane, kuma su ne kofofin Allah kuma tafarki zuwa gareshi, masu shiryarwa zuwa gare shi, su ne taskar iliminsa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma’ajiyar saninSa, don haka suka kasance aminci ga mazauna bayan kasa, kamar yadda taurari suke aminci ga mazauna sama kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S.A.W).
A wani hadisin yana fada: “Misalinsu a cikin wannan al’umma tamkar jirgin Annabi Nuhu (AS) ne wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka. Kuma ya zo a Kur’ani mai girma “Su sai dai bayin Allah ne ababan girmamawa, ba sa rigonsa da magana, kuma su da umarninsa masu aiki ne”. Surar Anbiya: 26-27. Kuma su ne wadanda Allah ya tafiyar masu da dauda ya tsarkake su tsarkakewa.
Mu mun yi imani da cewa umarninsu umarnin Allah ne, haninsu hanin Allah ne, biyayya gare su biyayya ce gare shi, saba musu kuma saba masa ne, kuma Soyayya gare su soyayya ce gare shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare Shi, bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayarwa ga Allah ne, kuma ya wajaba a mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu, da riko da maganganunsu.
Saboda haka mun yi imani da cewa hukunce-hukuncen Shari’ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta ba sai daga garesu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba ya samun nutsuwa da cewa ya bayar da wajibin da aka dora masa sai ta hanyarsu. Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S) ne duk wanda ya hau ya tsira, wanda kuwa ya jinkirta ya bar su ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da take makale da igiyoyin ruwan rikitarwa, da bata, da da’awoyi, da jayayya.
Bahasin imamanci game da tabbatar da cewa su ne halifofi na shari’a kuma masu shugabanci da izinin Allah a wannan zamanin ba shi ne muhimmi ba, wannan al’amari ne na tarihi da ya wuce, kuma tabbatar da shi ba zai sake dewo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari’a ba.
Abin da yake muhimmi shi ne abin da muka ambata na wajabcin komawa zuwa garesu wajan karbar hukunce-hukuncen shari’a, da kuma sanin abin da manzo (S.A.W) ya zo da shi kamar yadda ya zo da shi ta fuska ingantacciya.
Karbar hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu, kuma ba sa neman haskakawa daga haskensu, nisanta ne daga tafarkin daidai a Addini. Kuma baligi ba ya taba samun nutsuwar cewa ya sauke nauyin takalifin da ya hau kansa daga Allah, domin tare da samun irin wannan sabanin ra’ayoyi a tsakanin jama’ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari’a, sabanin da ba a sa ran dacewa a kansa, to fa babu wata dama ga baligi ya zabi mazhabar da ya ga dama ko ra’ayin da ya zaba, dole ne ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah (S.W.T) wajen ayyana mazhaba kebantacciya, wacce ya hakikance cewa da ita ce zai isa zuwa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ne zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abin da ake da yakinin wajabcinsa yana lizimta wajabcin samun yakinin sauke nauyinsa.
Dalili tabbatacce da yake nuna wajabcin koma wa Ahlul Baiti (A.S) da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan Annabi (S.A.W) sun hada da fadinsa (S.A.W): “Hakika Ni na bar muku abin da idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, Assakalaini, dayansu ya fi dayan girma; su ne littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa, da kuma Zuriyata Ahlin gidana, ku saurara ku ji, ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su riske ni a tafki”. [3]
Ka zurfafa tunaninka game da wannan hadisi mai girma zaka samu abin da zai gamsar da kai ya kuma girgizaka a wannan hadisin a ma’anarsa a fadinsa (S.A.W): “Matukar kun yi riko da su ba zaku taba bata ba a bayana har abada” abin da ya bar mana su ne sakalaini tare, ya kuma sanya su abubuwa guda biyu, bai wadatu da riko da daya ba, ba tare da dayan ba, da riko da su ne ba zamu taba bata ba har abada. Duba kuma ma’anar fadinsa (S.A.W) cewa: “Ba zasu taba rabuwa ba har sai riske ni a tafki” da nunin cewa wanda ya raba tsakaninsu bai yi riko da su a hade ba to ba zai taba samun shiriya ba har abada, don haka ne suka zama su ne; “Jirgin ruwan tsira” kuma “Aminci ga mazauna kasa” da duk wanda ya bar su, to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba, fassarar wannan da ma’anar soyayya gare su ba tare da riko da maganganunsu da bin tafarkinsu ba, gudu ne daga gaskiya da ba abin da yake kaiwa ga hakan sai bakin ra’ayin jahiliyya, da gafala daga tafarki madaidaici a fassarar bayanan zancen Larabci mai fasaha.

Son Ahlul Baiti (A.S)

Madaukaki ya ce: “Ka ce ni ba na rokon ku wani lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai”. Surar Shura: 23. Mun yi imani cewa bayan wajabcin riko da Ahlul Baiti (A.S), wajibi ne a kan kowane musulmi ya dabi’antu da sonsu da kaunarsu domin a ayar da aka ambata an takaita abin da ake nema daga mutane da nuna soyayyar makusantansa (A.S). Ya zo ta hanyoyi masu yawa da cewa; Son su alamar imani ne kin su kuma alamar munafinci ce, kuma duk wanda ya so su ya so Allah da manzonsa, wanda kuma ya ki su, to ya ki Allah da Manzonsa (S.A.W).
Hakika son su wajibi ne daga laruran addini da ba ya karbar jayayya ko kokwanto. Domin dukkan musulmi sun hadu a kan hakan duk da sabanin mazhabobinsu da ra’ayoyinsu, in ban da kadan daga wasu jama’a da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah wadanda aka sanya musu sunan “Nawasib” wato wadanda suka kulla gaba a kan Zuriyar Annabi (S.A.W), don haka ne ma ake kirga su a cikn masu inkarin abin da yake wajibi na addinin musulunci tabbatattu, wanda kuma yake karyata larurar Addini ana kirga shi a cikin masu karyata ainihin sakon musuluncin koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada, saboda haka ne kin Ahlul Baiti (A.S) ya zama daga alamomin munafunci son su kuwa ya zama daga alamomin imani kuma don haka ne kinsu ya zama kin Allah (S.W.T) da manzonsa (S.A.W).
Kuma babu shakka Allah (S.W.T) bai wajabta son su ba sai don su sun cancanci soyayya da biyayya ta bangaren kusancin su da Allah da manzonsa, da tsarkinsu, da nisantar su ga shirka da sabo, da kuma dukkan abin da yake nisantarwa daga karimcin ubangiji da yardarsa. Ba zai taba yiwuwa ba a suranta cewa; Ubangiji ya wajabta son wanda yake aikata sabo ko kuma wanda ba ya bin sa, domin shi ba shi da wata kusanci ko abotaka da wani, mutane a gurinsa ba komai ba ne sai bayi ababan halitta masu matsayi daya, kadai mafificinsu a gurin Allah shi ne mafi tsoronsu gareshi. Duk wanda ya wajabta son su a kan mutane baki daya to babu makawa ya zamanto mafi takawarsu, kuma mafi darajarsu baki daya, ba don haka ba, da waninsa ya fi cancantar wannan soyayyar, kuma da ya kasance kenan Allah yana fifita wasu mutane a kan wasu a wajabcin so da biyayya haka nan kawai ko da wasa ba tare da cancanta ko daraja ba.

Matsayin Imamai (A.S)

Mu ba mu yi imani ga Imamanmu (A.S) da abin da ‘Yan gullat [4] da ‘Yan Hululiyya [5] suka yi ba, “Kalmar da take fita daga bakunansu ta girmama”. Surar Kahf 5. Imaninmu game da su shi ne cewa su mutane ne kamarmu, suna da abin da yake garemu, kuma abin da ya hau kanmu ya hau kansu, sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa, Allah ya kebance su da karamarsa, kuma ya so su da soyayyarsa, domin suna da karamarsa, kuma ya ba su wilayarsa, domin su suna kan mafi daukakar daraja da ta dace da dan Adam na daga ilimi, da takawa, da jarumta, da karimci, da kamewa, da dukkan kyawawan dabi’u mafifita, da siffofi abin yabo, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abin da aka kebance su da shi.
Da wannan ne suka cancanci su zamo Imamai masu shiryarwa kuma makoma bayan Annabi a cikin duk abin da yake na addini na bayani da shar’antawa, da kuma abin da ya kebanta da Kur’ani na daga tafsiri da tawili.
Imaminmu Ja’afar Assadik (A.S) Ya ce: “Duk abin da ya zo muku daga gare mu daga abin da ya halatta bayi su siffanta da shi, ba ku kuma san shi ba, ba ku fahimce shi ba, to kada ku yi musun sa, ku mayar da shi gare mu, amma abin da ya zo muku daga garemu wanda bai halatta bayi su siffantu da shi ba, to ku yi musun sa kada ku mayar da shi zuwa gare mu.

Imamanci Sai Da Nassi

Mun yi imani cewa lmamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah madaukaki a harshen Manzonsa, ko harshen lmamin da ya aka sanya shi ta hanyar nassi idan yana son ya yi wasiyya da lmamin bayansa, hukuncin lmamanci a nan tamkar hukuncin annabci ne ba tare da wani bambanci ba, mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah ya ayyana mai shiryarwa ga dukkan mutane, kamar yadda ba su da hakkin ayyana shi, ko kuma kaddamar da shi, ko zabensa, domin mutumin da yake da tsarki da karfin daukar nauyin lmamanci baki daya, da kuma shiryarwa ga ‘yan Adam gaba daya, wajibi ne kada a san shi sai da shelantawar ubangiji, kuma ba a ayyana shi sai da ayyanawarsa.
Mun yi imani cewa Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da halifansa kuma shugaban talikai bayansa, sai ya ayyana dan amminsa Aliyyu Dan Abi Dalib Amiri ga musulmi, kuma amini kan wahayi, lmami ga halittu, ya ayyana shi a gurare da dama, kuma ya nada shi, kuma ya karba masa bai’a a kan shugabancin muminai ranar Gadir yana mai cewa: “A saurara a ji! Duk wanda na kasance shugabansa ne to wannan Ali shugabansa ne, Ya ubangiji! ka so wanda ya so shi, ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tozarta wanda ya tozarta shi, kuma Ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya’’.
Daga cikin wuraren farko da ya yi wasiyya da imamancin-sa akwai fadinsa yayin da ya kira danginsa makusanta ya ce: “Wannan shi ne dan’uwana, kuma wasiyyina, kuma halifana a bayana, ku ji daga gareshi ku bi shi”. A yayin nan kuma shi yana yaro bai balaga ba. Kuma ya maimaita fadinsa da yawa da cewa: “Kai a gare ni tamkar matsayin Haruna ga Musa ne, sai dai babu Annabi a bayana”. Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar:
"Kadai cewa Allah shi ne majibancinku da Manzonsa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka suna masu ruku’u". Surar Ma’ida: 55. Wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya yi sadaka da zobe yana cikin ruku’u. Wannan dan littafin ba zai iya bin diddigin dukkan abin da ya zo na daga ayoyin Kur’ani da ruwayoyi ko bayaninsu ba game da wannan maudu’i. [6]
Sannan shi ma ya yi wasiyya da Imamancin Imam Hasan da Imam Husain (AS), shi kuma Husain (A.S) ya yi wasiyya da imamancin dansa Aliyyu Zainul Abidin (AS), haka nan dai Imami ke bayar da wasiyyar imamin da zai zo bayansa har zuwa kan na karshensu kamar yadda zai zo.

Adadin Imamai

Mun yi imani da cewa Imamai wadanda suke da siffar Imamancin gaskiya su ne makomarmu a cikin hukunce-hukuncen shari’a, wadanda Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da su da sunayensu gaba daya, sannan wanda yake gabata yana wasiyya da mai biye masa kamar haka:


Adadi AI- kunya Suna Lakabi haihuwa Rasuwa 1 Abul Hasan Aliyyu Murtadha Shekara 23 K.H Shekara 40 H 2 Abu Muhammad Hasan Zakiyyi Shekara 2 H Shekara 50 H 3 Abu Abdullah Husain Shahid Shekara 3 H Shekara 61 H 4 Abu Muhammad Ali Sajjad Shekara 38H Shekara 95 H 5 Abu Ja’afar Muhammad Bakir Shekara 57 H Shekara 114 H 6 Abu Abdullah Ja’afar Sadik Shekara 83 H Shekara 148 H 7 Abu Ibrahim Musa Kazim Shekara 128 H Shekara 183 H 8 Abul Hasan Aliyyu Ridha Shekara 148 H Shekara 203 H 9 Abu Ja’afar Muhammad Jawad Shekara 195 H Shekara 220 H 10 Abul Hasan Aliyyu Hadi Shekara 212 H Shekara 254 H 11 Abu Muhammad Hasan Askari Shekara 232 H Shekara 260 H 12 Abul Kasim Muhammad Mahdi Shekara 256 H …..
Imam Al-Mahadi (AS) Shi ne Hujja a zamaninmu kuma boyayyen da ake sauraro, Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukaka mafitarsa, zai zo domin ya cika duniya da adalci bayan an cike ta da zalunci.

Imam Mahadi (A.S)

Hakika albishir da bayyanar imam Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Fadima (A.S) a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci ya tabbata daga Annabi (S.A.W) ta ruwayoyi masu yawa, kuma dukkan musulmi duk da sabanin mazahabobinsu sun ruwaito hadisai game da shi.
Fikirar samuwar imam mahadi (A.S) ba wani sabon abu ba ne da Shi’a suka kago shi saboda iza su da yaduwar zalunci ya yi zuwa gare shi, har suka yi mafarkin bayyanar wani wanda zai zo ya tsarkake kasa daga daudar zalunci, kamar yadda wasu masu neman kawo rikici da rudani marasa adalci suka raya. Ba don tabbatar akidar Mahadi (A.S) daga Annabi (S.A.W) ba, ta yadda dukkan musulmi suka san ta kuma ta kafu a zukatansu suka yi imani da ita, da masu da’awar mahadiyyanci a karnonin farko kamar kaisaniyya, da Abbasawa, da wasu daga Alawiyyawa, da sauransu, ba su iya yaudarar mutane ba ta hanyar samun dama da amfani da wannan akida wajen neman mulki da shugabaci, domin sun sanya da’awar mahadiyyancinsu ta karya ta zama hanyar tasiri a kan jama’a gaba daya da kuma shiga rayukan jama’a.
Mu tare da Imaninmu da ingancin Addinin musulunci, kuma cewa shi ne cikamakon addinan Ubangiji, kuma ba ma sauraron wani Addini da zai zo domin gyara dan Adam, hada da abin da muke gani na yaduwar zalunci da yawaitar fasadi a duniya, ta yadda ba zaka iya samun masakar tsinke ba ga adalci da gyara a kasashen duniya, tare da kuma abin da muke gani a fili na nesantar musulmi daga addininsu, da kuma ajiye hukunce-hukuncen musulunci da dokokinsa a gefe guda a dukkan kasashen musulmi, da kuma rashin lizimtuwarsu da koda daya daga dubban hukunce-hukuncensa, amma duk da haka ba makawa mu saurari budi da farin ciki da dawowar Addinin musulunci da karfinsa da iyawarsa wajan gyara wannan duniyar da ta dulmiya cikin takurawar zalunci da fasadi.
Sannan kuma ba zai yiwu ba musulunci ya dawo da karfinsa da jagorancinsa a kan dan Adam baki daya ba, alhalin yana kan wannan halin da yake ciki a yau da gabanin yau na daga sabanin mabiyansa a dokokinsa da hukunce-hukuncensa da ra’ayoyinsa game da shi, tare da wannan hali da suka samu kansu a ciki a yau da ma kafin yau na bidi’o’i da canje-canje a dokokinsa, da bata a cikin da’awoyinsu.
Na’am ba zai yiwu ba Addini ya koma ga karfinsa sai dai idan mai gyara babba ya jagorance shi, yana hada kansu, yana kuma rushe abin da aka raba masa na daga bidi’o’i da bata, tare da taimakon Ubangiji da ya sanya shi shiryayye mai shiryarwa, wanda yake da matsayi mai girma na Shugabanci na gaba daya, da kuma iko mai sabawa al’ada, domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
A takaice; Dabi’ar yanayin fasadi a duniyar dan Adam ta kai matuka a baci da kuma zalunci, duk da kuwa imani da ingancin wannan addini da cewa shi ne cikamakon addinai, wannan al’amari ya hukumta sauraron mai wannan gyara domin tseratar da duniya daga abin da take ciki. Saboda haka ne dukkan bangarorin musulmi suka yi imani da wannan sauraron, kai har da ma wadanda ba musulmi ba, sai dai kawai bambancin da yake tsakanin mazhabar Imamiyya da waninta shi ne, ita mazhabar imamiyya ta yi imani cewa wannan mai gyaran mutum ne ayyananne wanda aka haife shi a shekarar hijira ta 256, kuma bai gushe ba yana raye, kuma shi dan imam Hasan Askari ne mai suna “Muhammad” (A.S). Wannan kuwa saboda abin da ya tabbata daga Annabi (S.A.W) da kuma imamai (A.S) game da alkawarin zuwansa, da haihuwarsa, da boyuwarsa. Bai halatta ba Imamanci ya yanke a wani zamani daga zamuna koda kuwa Imami ya kasance boyayye ne, domin ya bayyana a ranar da Allah ya yi alkawari, wanda kuma wannan yana daga cikin asiran Ubangiji da babu wanda ya san su sai shi.
Kuma rayuwarsa da wanzuwarsa ba komai ba ne sai mu’ujiza ce da Allah ya sanya domin ba ta fi mu’ujizar kasancewarsa imami ga mutane yana dan shekara biyar ba a ranar da mahaifinsa ya koma zuwa ga Ubangiji Madaukaki, kuma ba ta fi Mu’ujizar Annabi Isa (A.S) girma ba da ya yi magana da mutane yana cikin shimfida yana jariri, kuma aka aike shi Annabi ga mutane.
Tsawon rayuwa fiye da dabi’a fannin likitanci bai musanta shi ba, kuma ba ya ganinsa mustahili, sai dai shi likitanci bai kai matsayin da zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba. Idan kuwa likitanci ya gajiya a kan haka to Allah mai iko ne a kan komai. Kuma tsawaita rayuwar Annabi Nuhu (AS) da wanzuwar Annabi Isa (AS) ya faru kamar yadda Kur’ani ya bayar da labari, idan kuwa mai shakka ya yi shakku game da abin da Kur’ani ya ba da Iabari game da shi, to sun yi hannun riga da Musulunci.
Yana daga abin mamaki musulmi ya tsaya yana tambaya game da yiwuwar haka alhalin yana da’awar imani da Littafi Mabuwayi.
Daga cikin abin da ya zama dole mu ambace shi a nan shi ne cewa; sauraron ba yana nufin musulmi su nade hannayensu game da al’amuran da suka shafi Addininsu ba ne, da kuma abin da ya wajaba na taimakonsa, da jihadi a tafarkinsa, da riko da hunkunce-hukuncensa, da yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Musulmi har abada abin kallafawa ne da aiki da abin da ya sauka na daga hukunce-hukuncen Shari’a, kuma ya wajaba a kansa ya yi kokarin sanin su ta fuska ingantacciya, kuma wajibi ne a kansa ya yi umarni da kyakkyawa, kuma ya yi hani da mummuna gwargwadon daidai yadda zai iya “Dukkanku makiyaya ne kuma kowannenku abin tambaya ne game da abin kiwonsa.” Saboda haka bai halatta gareshi ba ya takaita wajibansa don yana jiran mai kawo gyara Imam Mahadi (A.S), wanda yake mai shiryarwa da aka yi albishir da shi, domin wannan ba ya saryar da takalifin da aka kallafa, ba ya jinkirta aiki, ba ya sa mutane su zama karazube kamar dabbobi.


1. Fadinsa madaukaki: “Idan ma ba ku taimake shi ba to ai Allah ya riga ya taimake shi yayin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi yana na biyun su biyu yayin da suke cikin kogo yayin da yake cewa ma’abocinsa kada ka damu hakika Allah yana tare da mu, sai Allah ya saukar da nutsuwarsa gareshi ya kuma taimake shi da rundunoni da ba ku gan su ba, kuma ya sanya kalmar wadanda suka kafirta makaskanciya kalmar Allah kuma ita ce madaukakiya kuma lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima”. Surar Tauba: 40.
2. Kamar yadda yake a fadar Ubangiji “Ka ce: Ya Ubangiji Ka kara mini ilimi”. Surar Daha: 114.
3. Masu ruwaya a tafarkin Sunna da Shi’a sun hadu a kansa.
4. Masu fadin cewa imamai ubangizai ne ko kuma su ba ma mutane ba ne.
5. Masu imani da shigar Ruhin Ubangiji madaukaki jikin imamai.
6. Koma wa Littafin Sakifa na mawallafin wannan littafin domin karin bayani da sharhi ga wasu ayoyin kur’ani.Ra'ayinku

Suna :
Imel :
Rubuta Jimillar Lambobin a cikin akwatin nan
4+3 =